Sport
Dollar
38,6628
0.02 %Euro
44,0183
0.49 %Gram Gold
4.239,1500
1.35 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%"Nijar za ta iya dogaro kan IMF saboda muna da dangantaka mai kyau, musamman ta ɓangaren samar da rance da kuma juriya na ɗorewa [na lamurra]," in ji jami’in na IMF.
Firaminista kuma ministan tattalin arziki da na kuɗi na ƙasar Nijar, Ali Mahamane Lamine Zeine, ya gana da wata tawagar asusun ba da lamuni na duniya (IMF) game da inganta tattalin arzikin ƙasar.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar Nijar ya ruwaito cewa Firaministan ya karɓi baƙuncin tawagar ta IMF a ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban da ke lura da ɓangaren Afirka, Antonio David, a Yamai ranar Talata.
Kazalika kamfanin ya ambato Antonio David yana cewa ya “tattauna makomar tattalin arziƙin Nijar da kuma ƙaddamar da sauye-sauye domin tattara albarkatu domin inganta yadda ake kashe kuɗin ƙasa tare da inganta harkokin ‘yan kasuwa da kuma samun kuɗi [ na jari].”
“Mun kuma yi magana game da matakai na inganta bayyana gaskiya da kuma adalci a mulki da sauye-sauye domin ƙarfafa juriya game da firgicin yanayi,” kamar yadda kafanin dillancin labaran Nijar ya ambato shi yana cewa.
David ya ƙara da cewa "waɗannan tataunawar suna da inganci sosai kuma sun ba da ma’ana sosai."
“Nijar za ta iya dogaro kan IMF saboda muna da dangantaka mai kyau, musamman ta ɓangaren samar da rance da kuma juriya na ɗorewa [na lamurra],” in ji jami’in na IMF.
Waɗanda suka halarci zaman sun haɗa da shugaban hukumar kwaston da ma masu bai wa Firayim Ministan Shawara.
Comments
No comments Yet
Comment