Dollar

38,6432

0.04 %

Euro

43,8746

-0.21 %

Gram Gold

4.190,6400

-1.75 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

An shaida fashewar bama-bamai da tashin gobara a babban birnin ƙasar Port Sudan yayin da birnin ke fama da yaƙin basasa.

An ji ƙarar fashewar bama-bamai a birnin Port Sudan

An ji ƙarar fashewar bamaba-bamai a birnin Port Sudan mai tashar jiragen ruwa, a kwana na uku a jere yayin da dakarun RSF suka ƙaddamar da hare-hare a fadar gwamnatin sojin ƙasar.

Wani wakilin kamfanin dillancin labaran AFP ya ba da rahoton cewa an ji fashewar wani abu mai ƙara sosai da sanyin safiyar ranar Talata kuma an ga hayaƙi ya turnuƙe sararin samniya a tashar jiragen ruwa da ke birnin, inda ganau suka ba da rahoton fashewar wani abu a wani wurin adana kayayyaki.

Ganau a arewacin birnin sun ba da rahoton cewa an harba rokokin kakkaɓo jiragen sama daga wani sansanin soji.

Tun da farko dai, wani harin jirgi mara matuƙi a filin jiragen sama na Port Sudan ya hana jirage tashi, in ji wani jami’in filin jirgin.

"Jirgi mara matuƙin ya kai hari ne a yankin fararen-hula na filin jirgin saman," in ji jami’in da ya nemi a ɓoye sunansa, kwanaki biyu bayan sojin ƙasar sun ɗoura alhakin hari kan sansanin sojin filin jiragen saman kan rundunar RSF.

Hare-haren sun nuna ƙara tsananin yaƙi yayin da birnin da ke Bahar Maliya ya zama matattarar ayyukan jinƙai da wajen ya da zango da harkokin diflomasiyya da kuma fadar gwamnati mai alaƙa da soji wadda kafin wannan makon ba a kai masa hari na sama ko na ƙasa ba.

A ranar Lahadi ne hare-haren jirage mara matuƙi suka afka wa wani sansanin sojin da ke kusa da filin jiragen saman, filin jiragen sama ɗaya tilo mai aiki,

Kuma bayan haka ne aka kai hari kan rumbunar ajiyar mai a birnin.

A lamuran guda biyu, majiyoyin soji sun ɗaura alhakin kai hare-haren kan rundunar RSF wadda sojin ta shafe shekaru biyu tana yaƙi da ita.

Hare-haren sun zo ne bayan wata majiyar soji ta ce sojin ta lalata wani wurin ajiyar jirgin sama da makamai a filin jiragen saman Nyala da rundunar RSF ke da iko a kai.

 

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#