Dollar

38,5971

0.07 %

Euro

43,8359

0.45 %

Gram Gold

4.096,5400

1.93 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Wani gajeren bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta ya nuna yadda takalmin ya sami shugaban a kafaɗarsa ta hagu a lokacin da yake gudanar da jawabi.

An jefi shugaban Kenya William Ruto da takalmi yana tsaka da jawabi

An jefi Shugaban Kenya William Ruto da takalmi a lokacin da yake jawabi ga dandazon jama’a a garin Kehancha da ke yammacin ƙasar a ranar Lahadi.

Wani gajeren bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta ya nuna yadda takalmin ya sami shugaban a kafaɗarsa ta hagu a lokacin da yake gudanar da jawabi.

Babu wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasar kan wannan lamari zuwa lokacin buga wannan labarin.

Rangadi na kwana uku

Ruto ya soma rangadinsa na kwana uku a garin Migori da ke yammacin Kenya. Migori na da nisan kilomita 370 daga Nairobi babban birnin ƙasar.

Migory na da ƙawance sosai da ɓangaren ‘yan adawa, waɗanda ke ƙarƙashin jagorancin Raila Odinga, wanda bai samu nasara a kan Ruto ba a zaɓen Kenya da aka gudanar na shugaban ƙasa a shekarar 2022.

Odinga, wanda ya riƙe muƙamin firaministan Kenya daga 2008 zuwa 2013 tuni ya cim ma yarjejeniyar haɗin kai da Shugaba Ruto.

Gwamnatin shugaba Ruto da ke wa'adin mulkinta na farko na shekaru biyar, a lokuta da dama ta fuskanci adawa daga 'yan kasar Kenya, wadanda ke nuna rashin amincewarsu da ƙaruwar haraji da tsadar rayuwa, tun bayan hawan tsohon mataimakin shugaban kasar a kan karagar mulki a watan Satumban 2022.

 

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#