Dollar

38,6477

0.03 %

Euro

44,0288

0.06 %

Gram Gold

4.266,3900

0.03 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Daga abinci zuwa sauran kayan bukatun yau da kullum - tallafin jinƙai na Turkiyya na ci gaba da zuwa yankuna, tana tunatar da cewa rikici na iya raba kawuna, amma tausayi na hade su.

Jirgin ruwa na biyu ɗauke da kayan tallafi daga Turkiyya ya isa Sudan ana tsaka da yaƙi

Wani jirgin ruwan Turkiyya dauke da sama da tan 1,600 na kayan tallafin jinƙai ya isa Port Sudan, yana mika babban taimako a lokacin da kasar ke ci gaba da fuskantar rikicin jinƙai da ke bukatar gaggawa.

Jirgin ruwa da aka baiwa sunan “Jirgin Alheri” na biyu, ya bar Turkiyya karkashin kulawar Kungiyar Bayar da Agaji ta IHH ta Turkiyya, inda ya kai tan 1.605 na kayan abinci, tufafi, kayan tsafta da kayan sanar da dakunan zama. 

Bayan jirgin ya isa tashar ranar Litunin an yi masa tarba a hukumance, inda Jakadan Turkiyya a Khartoum Fatih Yildiz, mamban gudanarwa na IHH Mehmet Enes Arikan, Kwamishiniyar Ayyukan Jinkai a Sudan Selva Adem da sauran manyan jami’an gwamnati.

“Wannan ne jirgin ruwan Turkiyya na hudu dauke da kayan taimakon jinkai tun bayan fara rikici ,” Jakada Yildiz ya fada wa Anadolu. 

“Guda biyu sun ƙarƙashin kulawar Hukumar Tallafin Jinƙai ta Turkiyya (AFAD) inda wannan kuma ya zo karkashin kungiyar IHH.

Yildiz ya yi karin haske game da muhimmancin ayyukan, misali a yayin da rahotannin ingantar tsaro ke zuwa.

“Isowar wannan jirgi na faranta zukata - ba wai gare mu kawia ba, har ma ga jama’ar Sudan,” in ji shi. “A lokacin da ake kubutar da Khartoum, goyon bayanmu na nufin sama da kowanne lokaci.”

Arikan na IHH ya sake jaddada aniyar kungiyar na tallafawa Sudan a dogon zango, yana mai lura da cewa halin da ake ciki a yanzu a Sudan na ta’azzara tun 15 ga Afrilun 2023, lokacin da arangama ta balle tsakanin sojoji da mayakan RSF.

“Kokarinmu na ci gaba karkashin manufa mai taken ‘Alheri Ke Jagoranta, A Kan Hanyar Zuwa Sudan,” in ji Arikan. Muna da manufar isa ga wadanda ke da tsananin bukata, mu rarraba kayan tallafi tare da hadin gwiwa da mahukuntan yankunan da abokan ayyukan jinkai.”

Halin da ake ciki a Sudan

A ranar Talata, an jiyo karar fashewar wasu abubuwa a Port Sudan cibiyar rikicin kasar, rana ta uku a jere tun bayan da mayakan RSF suka fara kai hare-hare kan sojojin gwamnati.

Tun watan Afrilun 2023, mayakan RSF ke ta arangama da sojojin Sudan don kwace iko da babban birnin Khartoum, wanda ya janyo mutuwar dubunnan mutane da janyo rikicin jin kai mafi muni a duniya.

An kashe sama da mutane 20,000 tare da raba mutum miliyan 15 da matsugunansu, kamar yadda MDD da mahukuntan yankin suka bayyana.

Sai dai kuma binciken masana a Amurka ya yi hasashen cewa mutanen da aka kashe za su kai 130,000.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#