Sport
Dollar
38,7786
0.39 %Euro
43,8944
0.27 %Gram Gold
4.147,5900
1.06 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%A tsakiyar watan Afrilu, an tilasta wasu jiragen ruwa dauke da tan 1,000 na abinci da kuma sauran kayan abinci masu gina jiki da suka nufi jihar Upper Nile koma wa saboda rashin tsaro, in ji WFP da UNICEF.
Kusan wata guda kenan, yaƙi a gaɓar kogin Nilu a Sudan ta Kudu ya hana kai agajin jinƙai ga sama da yara 60,000 da ke fama da tsananin yunwa a arewa maso gabashin kasar, kamar yadda wasu hukumomin Majalisar Dinkin Duniya (MDD) biyu suka sanar a ranar
Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP) da kuma hukumar kula da kananan yara (UNICEF) sun ce suna sa ran soma kai abinci mai gina jiki ga jihar Upper Nile, wacce ke da mafi girman matsalar karancin abinci mai gina jiki a kasar a karshen watan Mayu.
"Yaran su ne sahun gaba waurin fama da wannan matsala a lokutan gaggawa, idan ba mu kai musu agaji cikin sauri ba, akwai yiwuwar matsalar ta yi kamari a yankunan da tuni suka fada cikin wannan yanayi’’ a cewar wakiliyar WFP a Sudan ta Kudu Mary- Ellen McGroarty a cikin wata sanarwar hadin gwiwa ta WFP da UNICEF.
Hanyar Kogin Nilu jigo ce wajen jigilar kayayyaki a Sudan ta Kudu saboda rashin wadatar hanyoyin kasa da na ruwa masu kyau, musamman a lokacin damina, inda ba a iya bin hanyoyi da dama.
Ko da yake dai, hukumomin ba su bayyana ko wane fada ne ya yi sanadiyar katse hanyar jirgin ruwan ba, amma dakarun gwamnati na ci gaba da fafatawa da ‘yan kabilar Nuer da aka fi sani da White Army a yankunan da ke kusa da Kogin Nilu tun a watan Maris.
Wannan rikici ya kai ga kama mataimakin shugaban kasar na farko Riek Machar da kuma rikicin siyasa da ya kunno kai, lamarin da ya sa MDD ta yi gargadin cewa ka iya sake dawo da mummunan yakin basasar da ya zo karshe a shekarar 2018.
A tsakiyar watan Afrilu, an tilasta wasu jiragen ruwa dauke da tan 1,000 na abinci da kuma sauran kayan abinci masu gina jiki da suka nufi jihar Upper Nile komawa saboda rashin tsaro, in ji WFP da UNICEF.
Hukumomin sun yanke shawarar hana sanya kayayyaki a cibiyoyin kiwon lafiya da ma'ajiyar kayayyaki a wuraren da ba su da tsaro saboda guje wa masu satar ganima, in ji su.
“Mun dan yi sanyin gwiwa wajen kai kayayyakin agaji saboda fargabar ba za su isa ga yaran da ke da matukar bukatarsu ba, sakamakon fada da sace-sacen da ake yi a hanyar kogin,” kamar yadda Obia Achieng, wakilin UNICEF ya shaida.
Comments
No comments Yet
Comment