Sport
Dollar
38,7399
-0.06 %Euro
43,5225
-0.29 %Gram Gold
4.084,0600
-1.44 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Ruwan saman da aka rinƙa sheƙawa ya ƙara wa ambaliyar ƙarfi, inda ruwan ya shafe gidaje da kuma katse hanyoyin sadarwa.
Aƙalla mutum 62 aka tabbatar da mutuwarsu sannan 50 suka ɓace bayan wata mummunar ambaliyar ruwa ta faru a ƙauyukan da ke gaɓar Tafkin Tanganyika a Kudancin Lardin Kivu da ke Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, kamar yadda hukumomi suka tabbatar a ranar Asabar.
Ambaliyar ta faru ne da misalin 5:00 na asuba agogon ƙasar a ranar Juma’a, kamar yadda shaidu suka tabbatar.
Ruwan saman da aka rinƙa sheƙawa ya ƙara wa ambaliyar ƙarfi, inda ruwan ya shafe gidaje da kuma katse hanyoyin sadarwa.
Ministan Lafiya na Kudancin Kivu Theophile Walulika Muzaliwa ya shaida wa kafar watsa labarai ta Arab News ta waya cewa an samu tsaiko wurin aikin ceton da ake gudanarwa.
Ya bayyana cewa akwai jagorori da sauran shugabannin ƙauyuka da ke wurin da lamarin ya faru inda ake gudanar da aikin ceton tare da su.
Ya bayyana cewa ƙungiyar bayar da agaji ɗaya tilo da ke wurin ita ce ƙungiyar Red Cross.
Wannan ambaliyar na zuwa ne makonni bayan irin wannan ruwan saman ya yi sanadin mutuwar mutum 33 a Kinshasa babban birnin ƙasar.
Abubuwan more rayuwa a fadin ƙasar sun lalace a cikin 'yan watannin nan, inda aikin agaji ke da wuya sakamakon rikicin da ake yi a yankin.
Fadan da ake gwabzawa tsakanin dakarun gwamnati da kungiyoyin masu dauke da makamai ya yi kamari a cikin watan Fabrairu, abin da ya kara dagula abin da Majalisar Dinkin Duniya ta kira daya daga cikin mafi munin rikicin jin kai a duniya.
Comments
No comments Yet
Comment