Sport
Dollar
38,7737
0.03 %Euro
43,1060
-1.25 %Gram Gold
4.023,0200
-2.91 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Tashar talabijin ta Aljeriya ta ruwaito cewa mutanen biyu suna aiki ne ƙarƙashin Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Faransa, a sashen Tsaron Cikin Gida, kuma sun “gaza bin ƙa’idojin doka” wajen shiga kasar Aljeriya.
Hukumomin Aljeriya sun kori wasu jami'an leken asirin Faransa biyu a ranar Lahadi, bisa zargin shiga kasar da “fasfon bogi na diflomasiyya,” wanda hakan ke nuna alamun ƙarin tsamin dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.
A cewar tashar talabijin ta Aljeriya wato Algeria International TV, wadda gwamnatin ƙasar ke kula da ita, an bayyana cewa mutanen biyu suna aiki ne ƙarƙashin Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Faransa, a sashen Tsaron Cikin Gida, kuma sun “gaza bin ƙa’idojin doka” wajen shiga kasar Aljeriya.
Tashar ta bayyana wannan lamari a matsayin wata “dabara” da Ministan Harkokin Cikin Gida na Faransa, Bruno Retailleau, ya shirya.
Babu wani tsokaci daga hukumomin Faransa kan wannan korar da aka yi.
Rashin jituwa tsakanin ƙasashen biyu
Wannan lamarin ya biyo bayan korar ma’aikatan ofishin jakadancin Faransa guda 12 da Aljeriya ta yi a farkon watan Afrilu, a matsayin martani ga kama wani ma’aikacin ofishin jakadancin Aljeriya a birnin Paris bisa zargin hannu a sace wani mai adawa da gwamnatin Aljeriya.
Daga bisani, Faransa ta mayar da martani ta hanyar korar jakadun Aljeriya guda 12 tare da janye jakadanta daga Aljeriya domin yin shawara.
Wadannan matakan na martani sun biyo bayan wani ɗan ƙwarya-ƙwaryar sassauci da aka samu, bayan wata tattaunawa ta waya tsakanin Shugaban Aljeriya Abdelmadjid Tebboune da takwaransa na Faransa, Emmanuel Macron, a karshen watan Maris, da kuma ziyarar Ministan Harkokin Turai na Faransa, Jean-Noel Barrot, zuwa Aljeriya a ranar 6 ga Afrilu, inda ɓangarorin biyu suka yi alƙawarin farfaɗo da hanyoyin hadin gwiwa tsakanin ƙasashen.
Dangantakar diflomasiyya tsakanin Aljeriya da Faransa na ci gaba da kasancewa mai cike da ruɗani, musamman saboda matsalolin da ba a warware ba da suka samo asali daga mulkin mallakar da Faransa ta yi wa Aljeriya daga shekarar 1830 zuwa 1962.
Comments
No comments Yet
Comment