Dollar

38,7512

-0.03 %

Euro

43,5691

-0.23 %

Gram Gold

4.075,8200

-1.64 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Gwamnatin ta Nijar ta haramta fitar da shanu da raguna da awaki da raƙuma gabannin Babbar Sallah domin daƙile irin yadda farashinsu ke tashin gwauron zabi.

Gwamnatin Nijar ta haramta fitar da dabbobi daga ƙasar gabanin Sallar Layya

Gwanatin Sojin Nijar ta haramta fitar da dabbobi daga ƙasar gabanin Babbar Sallah, kamar yadda ma’aikatar cinikayya ta ƙasar ta bayyana.

Gwamnatin ta ce ta ɗauki wannan matakin ne domin daƙile tashin gwauron zabi da farashin dabbobin ke yi a duk lokacin sallah.

Ministan Cinikayya na Nijar Abdoulaye Seydou ya kuma ƙara da cewa babban dalilin ɗaukar wannan matakin na haramta fitar da shanu da raguna da awaki da raƙuma shi ne “tabbatar da wadatarsu” a kasuwanni gabannin shagalin bikin Sallah.

Ministan ya ce tuni aka bai wa jami’an tsaro umarnin aiwatar da wannan doka da kuma daƙile duk wanda ya yi yunƙurin karyata.

Fiye da kaso 90 na jama’ar Nijar Musulmai ne kuma suna yanka dubban dabbobi a lokacin sallar layya.

Sai dai a halin yanzu ƙungiyoyin ‘yan ta’adda na yawan satar dabbobi, lamarin da ke sa makiyaya na guduwa daga ƙauyukansu, a ƙarshe kuma dabbobi su ƙara tsada.

Satar dabbobin na daga cikin hanyoyin da ‘yan ta’addan ke samun kuɗin shiga inda mayaƙa musamman na Boko Haram ke sayar da dabbobin da suka sata domin samun kuɗin gudanar da ayyukansu na ta’addanci.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#