Sport
Dollar
38,8031
0.06 %Euro
43,4371
0.9 %Gram Gold
4.044,9200
0.24 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Ɗan wasan Nottingham Forest, Taiwo Awoniyi ya samu rauni lokacin da ya yi taho-mu-gama da turken raga a wasan da Nottingham Forest ta buga da Leicester ranar Lahadi.
Rahotanni daga ƙungiyar Nottingham Forest ta Ingila na cewa an yi wa ɗan wasan gaba na ƙungiyar, Taiwo Awoniyi tiyata a mararsa.
An garzaya da ɗan wasan ɗan asalin Nijeriya zuwa asibiti cikin gaggawa bayan ya samu rauni a ƙasan ciki, lokacin da ya bugi turken raga yayin wasan Nottingham Forest da Leicester City da aka tashi da ci 2-2.
An buga wasan ne a filin wasa na City Ground, gidan Forest a ranar Lahadi 11 ga Mayu 2025.
Awoniyi ya yi ƙoƙarin kai ƙafa don karɓar ƙwallon da Anthony Elanga ya bugo, amma bai samu nasara ba. Duk da haka, ya ci gaba da buga wasan bayan ya samu kulawar jami’an lafiya tsawon mintuna.
Sai dai ba a fahimci girman raunin ba sai ranar Litinin lokacin da likitocin Nottingham Forest suka duba ɗan wasan da kyau.
Daga nan ne aka yi gaggawar garzayawa da shi asibiti don masa tiyata, inda rahotanni suka ce raunin ba mai barazana ga rayuwarsa ba ne.
Martani mai zafi
Lamarin jin raunin ya jawo martani mai zafi daga mamallakin ƙungiyar Nottingham Forest, Evangelos Marinakis, wanda ya shiga filin wasan cikin fushi ya yi magana da kocin kungiyar, Nuno Espirito Santo, bayan tashi daga wasan.
Marinakis ya bayyana damuwarsa game da halin da Awoniyi ya shiga, musamman ganin cewa an bar shi ya ci gaba da wasa duk da cewa Nuno ya tuntuɓi likitocin ƙungiyar a mintunan ƙarshen wasan.
Wasan dai ya kasance mara daɗi ga Nottingham Forest, saboda burinsu na shiga gasar Zakarun Turai ya samu cikas, sakamakon canjaras da suka yi da Leicester, wadda ta riga ta sauka daga gasar Firimiya.
Ƙungiyar na matsayi na bakwai a teburin Firimiya, kuma a yanzu ba su da cikakken iko kan makomarsu, a ƙoƙarinsu na samun gurbin buga gasar Zakarun Turai ta baɗi, wanda zai zama karo na farko tun kakar 1980-81.
Wasa a Turai
Nottingham Forest na da tazarar maki ɗaya kacal daga rukunin biyar ɗin saman teburi a gasar Firimiya, wanda ke tabbatar musu da gurbin shiga ɗaya cikin gasannin Zakarun Turai.
A yanzu saura wasanni biyu a kakar bana, inda za su kara da West Ham da kuma Chelsea, wadda ke cikin manyan ƙungiyoyi biyar a Ingila.
Duk da haka, Forest sun riga sun tabbatar da samun gurbi a gasar UEFA Conference League, wanda zai ba su damar buga wata gasar Turai karo na farko tun kakar 1995-96.
Comments
No comments Yet
Comment