Dollar

41,4557

0.14 %

Euro

48,7133

-0.53 %

Gram Gold

4.977,1500

-0.64 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Kazalika sanawar ta ce Mai Shari’a Baffoe-Bonnie ya ba da gudunmawa mai yawa a fannin shari’ar Ghana.

Shugaba Mahama ya gabatar da sunan Paul Baffoe-Bonnie a matsayin alƙalin alƙalan Ghana

Shugaban Ghana John Mahama ya gabatar da sunan Paul Baffoe-Bonnie ga majalisar magabata ta ƙasar a matsayin alƙalin alƙalan Ghana kamar yadda sashi na 144(1) ya tanada.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ambato wata sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Felix Kwakye Ofosu, ya fitar na cewa mai shari’a Baffoe-Bonnie ya yi aiki tuƙuru bisa gaskiya a alƙalancin da ya yi a babbar kotu da kotun ɗaukaka ƙara da wanda yake a kotun ƙoli a yanzu.

Kazalika sanawar ta ce Mai shari’a Baffoe-Bonnie ya ba da gudunmawa mai tarin yawa a fannin shari’ar Ghana.

Mai magana yawun shugaban ya ce ilimi da rashin son kansa ya sa ana girmama shi a ɓangaren alƙalai da lauyoyi da ma fannin shari’a gaba ɗaya.

Ya ce ƙwarewarsa da kuma daɗewarsa a alƙalanci sun sa ya cancanta sosai ya riƙe kujerar alƙalin alƙalan ƙasar.

Kazalika sanarwar ta ce alƙalin alƙalan ya fara aiki ne a matsayin muƙaddashin alƙalin alƙalan ƙasar tun ranar 22 ga wata Afrilu.

 

Korar alƙaliyar alƙalan Ghana

A farkon wannan watan ne Shugaba Mahama ya kori alƙaliyar alƙalan ƙasar Gertrude Araba Esaaba Sackey Torkornoo, daga muƙaminta.

Shugaban ya sauke alƙaliyar ne bayan an same ta da laifin yin amfani da matsayinta wajen aikata ba daidai ba.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ruwaito cewa Shugaba Mahama ya ɗauki matakin ne bayan ya dogara kan sashe na 146(9) na kundin tsarin mulkin ƙasar na shekarar 1992.

Wannan ya biyo bayan samun sakamakon binciken kwamitin da aka kafa a ƙarƙashin sashe na 146 (6) na kundin tsarin mulkin ƙasar domin bincike kan ƙorafin da wani ɗan ƙasar ta Ghana mai suna Mista Daniel Ofori ya shigar a kan alƙaliyar alƙalan.

Wata sanarwa da Mista Felix Kwakye Ofosu, mai magana da yawun shugaban ƙasar kuma ministan sadarwar gwamnati ya sanya wa hannu a Accra, a babban birnin ƙasar  ta ce shugaban ƙasar ya ɗauki wannan matakin ne bayan kwamitin ya tabbtar da dalilin cire ta daga muƙaminta.

Ranar Litinin ne dai Shugaban ƙasar ya karɓi rahoton kwamitin da ya yi nazari kan ƙarar neman a kori alƙaliyar alƙalai Gertrude Araba Esaaba Sackey Torkornoo.

Maisharia Gabriel Scott Pwamang na kotun ƙolin ƙasar da ya jagoranci kwamitin ne ya gabatar da rahoton kwamitin ga shugaban ƙasar a fadar gwamnatin ƙasar da ke Accra.

 

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#