Dollar

41,3992

0.26 %

Euro

48,7139

-0.17 %

Gram Gold

4.864,5100

0.54 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Bayanai daga hukumomin Nijar sun ce an ɗauki wannan mataki ne a ƙoƙarin gwamnatin na kawo ƙarshen shekaru da aka shafe na rashin tsari a fannin tsaro da ke da matuƙar muhimmanci.

Gwamnatin Nijar ta rufe kamfanonin tsaro masu zaman kansu 400

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta rufe kamfanonin samar da tsaro masu zaman kansu 400 a lokaci ɗaya ta hanyar wata doka da ministan tsaron cikin gida Manjo Janar Mohamed Toumba ya rattaba wa hannu.

Bayanai daga hukumomin Nijar sun ce an ɗauki wannan mataki ne a ƙoƙarin gwamnatin na kawo ƙarshen shekaru da aka shafe na rashin tsari a fannin tsaro da ke da matuƙar muhimmanci.

Duk da cewa sanarwar ministan ba ta ba da hujja kan rufe kamfanonin ba, kafar watsa labarai ta Actu Niger ta ce an ɗauki matakin domin tsaftace tsarin samar da tsaron ƙasar.

Tun ranar 10 ga watan Yunin shekarar 2024 ne ma’aikatar tsaron cikin guda ta janye lasisi aikin kamfanoni uku na samar da tsaro: Securicom da GADNET Sécurité da kuma Manga Sécurité bayan sun nuna gazawa wajen gudanar da ayyukansu.

A hanlin yanzu waɗannan kamfanonin na cikin kamfanoni 400 da aka rufe har abada.

Yayin da wasu ke ganin wannan matakin a matsayin abin da zai janyo damuwa game da rashin ayyukan yi ga masu gadi, wasu na ganin matakin a matsayin abin da ake buƙata domin magance wani yanayi na rashin tabbas.

Ma’aikata da dama sun soki tsarin albashi da bai kai ya kawo ba da waɗannan kamfanoni ke bayarwa, wanda galibi bai kai 50,000 CFA  ba a ko wane wata, da kuma shafe sa’o’i masu yawa a aiki da rashin kariya kan matsalolin rayuwar yau da kullum.

 Dokar watan Fabrairun shekarar 2025

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#