Sport
Dollar
41,2832
-0.05 %Euro
49,0052
0.78 %Gram Gold
4.895,2200
0.21 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Fiye da iyalai 21,000 a Sudan ne ambaliyar ruwa da mamakon ruwan sama ya jawo ta shafa a jihohi 11 na kasar tun watan Yuni, kamar yadda hukumomi suka sanar a ranar Litinin.
Fiye da iyalai 21,000 a Sudan ne ambaliyar ruwa da mamakon ruwan sama ya jawo ta shafa a jihohi 11 na kasar tun watan Yuni, kamar yadda hukumomi suka sanar a ranar Litinin.
A cikin wata sanarwa da ma'aikatar lafiya ta Sudan ta fitar ta ce jihohin Al-Jazirah da Al Qadarif sun fuskanci ambaliyar ruwa a wannan makon, wadda ta shafi iyalai 3,639 (mutane 18,195).
Wannan ya sa adadin iyalai da abin ya shafa ya kai 21,811 (mutane 113,723) a tsakanin 30 ga watan Yuni zuwa 14 ga Satumba, a cewar sanarwar.
Ta kara da cewa lamarin ya shafi jihohi 11 daga cikin 18 na kasar Sudan da suka haɗa da: Al Qadarif, Kassala da Red Sea (gabas); Arewa da Kogin Nilu (arewa); Sennar da Blue Nile (kudu maso gabas); Kordofan ta Yamma da ta Arewa (tsakiyar yamma); Darfur ta Tsakiya (yamma); da Al-Jazirah (gabas-ta tsakiya).
Comments
No comments Yet
Comment