Dollar

41,3970

0.08 %

Euro

48,6749

-0.05 %

Gram Gold

4.844,4300

0.33 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Ko a kwanakin baya sai da sojojin Nijar 10 suka rasu yayin arangama da 'yan ta'adda a kusa da Burkina Faso.

An kashe sojojin Nijar 14 a wani harin kwanton-ɓauna a Tillaberi

Sojoji 14 na Nijar sun rasa rayukansu a ranar Laraba, 10 ga Satumba, a wani mummunan kwanton-ɓauna da ‘yan ta’adda ta yi wa dakarun rundunar tsaron ƙasa ta Nijar (FDS) da ke aikin Operation Al Mahaou.

An tura dakarun ne zuwa gaɓar hagu ta Kogin Nijar bayan samun rahoton sirri kan cewa wasu ’yan bindiga a kan babura guda biyar suna ƙoƙarin satar dabbobin al’umma. Da farko, sojojin sun yi nasarar ƙwato dabbobin tare da bin maharan. Sai dai wannan bin da suka yi wa maharan ya zama tarkon da aka shirya don yi musu kwanton-ɓauna

A cewar rahoton mako-mako na FDS kan ayyuka na musamman da dabarun yaki, kusan babura 50 ɗauke da ‘yan ta’adda suka yi wa sojojin kwanton-ɓauna. An yi musayar wuta mai tsanani, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji 14, yayin da biyu suka jikkata aka kuma garzaya da su wurin jinya.

A cikin wata sanarwa, Ministan Harkokin Ƙasa Tsaron Ƙasa, wanda ya yi magana a madadin Shugaban Ƙasa kuma Babban Kwamandan Sojoji, ya bayyana ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu da kuma rundunar tsaro baki ɗaya. Ya kuma yi addu’ar samun lafiya cikin gaggawa ga waɗanda suka jikkata.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#