Sport
Dollar
41,3970
0.08 %Euro
48,6749
-0.05 %Gram Gold
4.844,4300
0.33 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Kwamitin Kula da Bayar da Kariya ga Ambaliya a Nijar ne ya tabbatar da waɗannan alƙaluma a yayin taronsa na huɗu da aka gudanar a ranar Juma’a, 12 ga Satumbar 2025 a ɗakin taro na ofishin Firaminista.
Jumullar mutum 246,228 ne da kuma gidaje 32,251 ambaliyar ruwa ta shafa a Jamhuriyar Nijar sakamakon ruwan saman da aka fara tun daga farkon damina.
Kwamitin Kula da Bayar da Kariya ga Ambaliya a Nijar ne ya tabbatar da waɗannan alƙaluma a yayin taronsa na huɗu da aka gudanar a ranar Juma’a, 12 ga Satumbar 2025 a ɗakin taro na ofishin Firaminista.
A cewar kwamitin, zuwa yanzu, ambaliyar ta shafi unguwanni da ƙauyuka 1,009 a cikin ƙananan hukumomi 122, yayin da “tallafin da aka bayar zuwa 2 ga Satumbar 2025 ya kai ga gidaje 18,962 da suka ƙunshi mutum 142,642 tare da tan 1,896.2 na hatsi a cikin tallafin da aka bayar sau uku”.
“An bayar da umarni na musamman domin tabbatar da cewa tallafin ya kai ga waɗanda suke da bukatarsa,” in ji majiyar.
Comments
No comments Yet
Comment