Sport
Dollar
41,3970
0.08 %Euro
48,6749
-0.05 %Gram Gold
4.844,4300
0.33 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Hukumar Leken Asiri da Tsaro ta Somaliya (NISA) ta sanar da cewa dakarunta sun kashe Mohamed Abdi Dhiblaawe Afrax, wani babban kwamandan ƙungiyar Al-Shabaab.
Hukumar Leken Asiri da Tsaro ta Somaliya NISA ta sanar da cewa dakarunta sun kashe Mohamed Abdi Dhiblaawe Afrax, wani babban kwamandan ƙungiyar Al-Shabaab, a wani samame da suka shirya yi a Ugunji, da ke yankin Lower Shabelle.
Hukumar ta NISA ta tabbatar da cewa Afrax ne ya shirya yunkurin kisan gillar da bai yi nasara ba a kan ayarin motocin Shugaban Ƙasar Somaliya, Hassan Sheikh Mohamud a ranar 18 ga Maris ɗin 2025.
Harin 18 ga Maris na 2025
Da misalin ƙarfe 10:32 na safiyar ranar ne aka kai wa ayarin motocin shugaban hari a kusa da mahadar El-gaabta da ke gundumar Xamar-Jajab, a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama domin tafiya tare da dakarun sa-kai na Hirshabesha.
Daya baya ma’aikatar yada labaran ƙasar ta tabbatar da cewa an daƙile harin, kuma shugaban ya isa inda ya yi niyyar zuwa.
Comments
No comments Yet
Comment