Sport
Dollar
41,2717
0.05 %Euro
48,4417
-0.26 %Gram Gold
4.836,4900
0.28 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Hukumar COHO wadda aka kafa a shekarar 2013, ita take da alhaƙin shirya da sa ido da kuma jagoran lamuran aikin hajji da Umra a Nijar.
Hukumar Kula da Aikin Hajji da Umra ta ƙasar Nijar (COHO) ta buɗe rajistar Aikin Hajji ga maniyyata Hajji da Umra na shekarar 2026 a kan manhajarta ta GAHO.
"Hukumar Kula da Aikin Hajji da Umra (COHO) na sanar da masu ruwa da tsaki a Aikin Hajji (shugabannin kamfanonin Aikin Hajji da maniyyata da sauransu) cewa an buɗe manhajar GAHO domin rajistar maniyyatan Hajjin 2026/1447 ranar Asabar, 6 ga watan Satumban 2025 da ƙarfe 12 na rana.
“Sannan za a rufe ta ranar 30 ga watan Nuwamban 2025 da misalin ƙarfe 6 n yamma, wani wa’adin da ba za a sauya ba," in ji hukumar COHO a wata sanarwa.
Comments
No comments Yet
Comment