Dollar

41,2881

0.07 %

Euro

48,4049

0.04 %

Gram Gold

4.772,4800

0.35 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

An kai hare-haren ta sama ne sabbin maɓoyar 'yan ta’adda da aka gano a Zuwa, dajin Sambisa da ke Arewa maso-gabashin Nijerya, in ji hukumomi a ranar Alhamis.

Sojojin Nijeriya sun kashe ‘yan ta’addar Boko Haram 15 a maɓoyarsu da ke Dajin Sambisa

Rundunar Sojin Saman Nijeriya (NAF) ta kashe 'yan ta'addar Boko Haram sama da 15 a yankin Zuwa da ke dajin Sambisa a arewa maso gabashin Nijeriya, kamar yadda wani jami'i ya bayyana a ranar Alhamis.

Rundunar ta kashe 'yan ta'addar Boko Haram sama da 15 a ranar Larabar da ta gabata a wani bangare na Farmakan Hadin Kai na Hadin Gwiwa da rundunar hadin gwiwa ke kai wa a yankin Arewa maso Gabas, a cewar sanarwar da kakakin rundunar sojin sama, Ehimen Ejodame ya fitar.

Ya kara da cewa harin da aka kai ta sama ya nuna ingancin samun inda aka nufa, ƙarfin isa da kuma azama wajen yaƙi da ta’addanci.

"A ranar 3 ga Satumban 2025, wani shiri na tsanaki da aka aiwatar ya nufi wata sabuwar maboyar 'yan ta'adda da aka gano a yammacin Zuwa da ke Dajin Sambisa."

‘An rushe muhimman matsugunai da yawa’

"Bayan samun ingantattun bayanan sirri da sanya idanu da aka tabbatar, hare-haren sun nufi maboyar mayaka da kwamandojin da ke da alhakin tashe-tashen hankula a kwayen Bitta."

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#