Sport
Dollar
41,3970
0.08 %Euro
48,6749
-0.05 %Gram Gold
4.844,4300
0.33 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%An dai shirya fara yajin aikin ne da tsakar daren ranar Talata 16 ga watan Satumba, sannan kuma a kare a ranar Laraba 17 ga watan Satumba da karfe 11:59 na dare.
Ma’aikatan gidan radiyon gwamnatin Nijar, Rediyo-Télévision du Niger (RTN), sun fitar da sanarwar shiga yajin aiki na sa’o’i 48 domin nuna adawa da rashin tsaro da kuma neman a inganta yanayin aiki.
A cikin wata wasika mai ɗauke da kwanan watan 10 ga Satumban 2025, wasu ƙungiyoyi da wakilan ma’aikatan kafar sun bayyana cewa ba su da wani zaɓi illa su tashi tsaye su ɗauki wannan mataki, suna masu kwatanta yanayin da su ke ciki da “abin takaici” wanda ya tura ma’aikata “cikin talauci da rashin tsaro.”
An dai shirya fara yajin aikin ne da tsakar daren ranar Talata 16 ga watan Satumba, sannan kuma a ƙare a ranar Laraba 17 ga watan Satumba da karfe 11:59 na dare.
Babban abin da suke buƙata shi ne a gaggauta aiwatar da ƙarin sabon albashin da kwamitin gudanarwa na RTN ya amince da shi a watan Disamban 2024 wanda kawo yanzu ba a aiwatar da shi ba balle a soma biya.
Kazalika ƙungiyoyin sun yi ƙorafi kan rashin amincewarsu da jinkirin biyan albashin ma’aikata tare da yin kira da a warware basussukan da ake bin su don rage wa iyalai matsalar kuɗaɗe.
Baya ga batun albashi, ma'aikatan sun koka kan barazanar rayuwa a RTN wanda a cewarsu ke cikin haɗari.
Comments
No comments Yet
Comment