Sport
Dollar
41,2870
-0.02 %Euro
48,9539
0.71 %Gram Gold
4.900,7500
0.33 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Sun buƙaci hukumar gidan kallo na Silverbird da duk masu ɗaukar nauyin shirin da su janye, suna masu gargaɗin cewa rashin yin hakan zai haifar da ƙaurace wa bikin.
Wata babbar gamayyar ƙungiyoyin ‘yan Ghana da ke ƙasashen waje ta kusan mutane 400 da wasu ƙungiyoyi, sun yi kira da a soke bikin Fina-Finan Isra'ila da aka shirya gudanarwa a Silverbird Cinema, da ke Accra Mall a Ghana daga ranar 16 zuwa 20 ga Satumban 2025.
Matakin hakan na cikin wata sanarwa da suka fitar a ranar Litinin, inda masu fafutukar suka bayyana bikin a matsayin "wata farfaganda ta masu tsananin son kafa kasar Isra’ila" da nufin wanke "kisan ƙare dangi da wariyar launin fata na Isra’ila" a yayin da ake ci gaba da tashin hankali a Gaza.
Sun buƙaci hukumar gidan kallo ta Silverbird da duk masu ɗaukar nauyin shirin da su janye, suna masu gargaɗin cewa rashin yin hakan zai haifar da ƙaurace wa bikin.
Gamayyar ƙungiyoyin sun yi zargin cewa, tarihin Ghana na gwagwarmayar ƙin jinin mulkin mallaka da haɗin- gwiwa da masu fafutukar ƙwato 'yancin kai ya sa bikin ya zama cin zarafi kai-tsaye ga ƙimar ƙasa.
"Ba za mu iya tsayawa muna kallo ba, yayin da ake bayyana kisan kiyashin da ake yi wa Falasdinawa ta hanyar fasaha da al'adu.
“A ko yaushe Ghana na tsayawa a bangaren wadanda aka zalunta, kuma a yau dole ne mu tsaya tare da Falasdinu," in ji sanarwar.
Comments
No comments Yet
Comment