Dollar

41,2956

0.14 %

Euro

48,9383

-0.1 %

Gram Gold

4.868,1100

-0.5 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Harbe-harben sun faru ne ranar Litinin a jihar Tillaberi, kusa da Burkina Faso da Mali, inda ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi da ke da alaƙa Al-Qaeda da kuma ƙungiyar IS ke aika-aika.

‘Yan bindiga sun kashe mutane da dama a wurin bikin baftisma a Nijar

‘Yan bindiga bisa babura sun harbe aƙalla mutane 22 a wani ƙauye a yammacin Nijar, inda yawancinsu ke halartar wani bikin baftisma, kamar yadda kafofin watsa labaran ƙasar da wasu majiyoyi suka bayyana ranar Talata.
Sun kai hari ne ranar Litinin a Jihar Tillaberi, kusa da kan iyakar Burkina Faso da Mali, inda ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi da ke da alaƙa Al-Qaeda da kuma ƙungiyar IS ke aika-aika.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa an kashe mutum 15 ne daga farko a bikin baftisma a ƙauyen Takoubatt.
“Kana maharan suka nufi wajen ƙauyen Takoubatt inda suka kashe wasu mutane bakwai,” in ji mazaunin garin, wanda ya nemi a sakaye sunansa saboda dalilai na tsaro.
Wani gidan talabijin a ƙasar Elmaestro TV ya ba da rahoto kan “kisan mutum 22 da basu ji ba basu gani ba”.
“A wannan lokacin ma, Jihar Tillaberi ta sake cin karo da rashin tausayi, lamarin da ya jefa iyalai da ba su da laifi cikin jimami,” kamar yadda wani mai fafatukar kare ‘yancin ɗan’adam a Nijar Maikoul Zodi ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.
Shugabannin sojin Nijar suna ƙoƙarin daƙile hare-haren ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi a Tillaberi, inda suka girke dakaru masu yawa a yankin.
Kimanin sojoji 20 aka kashe a yankin a makon jiya.
Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Human Rights Watch ta yi kira ga hukumomin Nijar su ƙara ƙoƙari wajen kare fararen-hula daga hare-hare.
Ƙungiyar ta yi ƙiyasin cewa ƙungiyoyin ta’addancin sun yi wa mutanen ƙauye da masallata 127 kisan gilla a hare-hare biyar da suka kai a Tillaberi tun watan Maris.
A halin yanzu kuma, wata ƙungiya mai zaman kanta ACLED, wadda ke bibiyar waɗanda rikici ya rutsa da su a duniya, ta ce an kashe kimanin mutum 1,800 a Nijar tun watan Oktoba na shekarar 2024 — kashi uku cikin huɗu na kashe-kashen a Tillaberi aka aikata su.
Nijar da maƙwabtanta, Burkina Faso da Mali, waɗanda su ma sojoji da suka yi juyin mulki, sun kori sojojin Amurka da na Faransa da ke taya su yaƙi da ‘yan ta’adda.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#