Dollar

41,4559

0.14 %

Euro

48,6999

-0.54 %

Gram Gold

4.976,6200

-0.66 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Recep Tayyip Erdogan da matarsa Emine Erdogan sun halarci liyafar musamman da shugaban Amurka Trump da matarsa Melania suka shirya.

Shugaba Erdogan ya halarci liyafar musamman da Trump ya shirya wa shugabannin duniya a New York

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya halarci liyafar cin abincin dare ta musamman da shugaban Amurka Donald Trump da mai ɗakin shugaban ƙasar Melania Trump domin karrama shugabannin ƙasashe da matansu ranar Talata.

Matar Erdogan Emine Erdogan ce ta raka shi zuwa liyafar, wadda aka yi otel ɗin Lotte Palace a gefen taron MDD na 80 da aka yi a birnin New York.

Ba a bar ‘yan jarida su shiga zaman karramawar ba.

A gefe guda, Emine Erdogan, wadda ita ce shugabar kwamitin MDD mai ba da shawara game da kawar da shara, ta halarci wata liyafa da Melania Trump ta shirya wa matan shugabanni.

Taron ya ba da damar tattaunawa tsakanin masu ɗakin shugabannin ƙasashe.

A lokacin liyafar, an ga Emine Erdogan tana magana da wasu matan shugabannin ƙasashe kuma suke musayar ra’ayi kan batutuwa ciki har da yara da mata da yanayi da al’ada.

A wani ɓangare na daban, Emine Erdogan ta haɗu da Zita Oligui Nguema, mata ga shugaban ƙasar Gabon Shugaba Brice Clotaire Oligui Nguema, a gidan Turkiyya (Türkevi).

A lokacin ganawar, Nguema ta bayyana fatanta na samun ƙwarin gwiwa daga shirin "kawar da shara " domin ta haɗa kai da Turkiyya a wannan fannin.

Bisa ga abin da Nguema ta nema, Erdogan ta ce za a iya samar da horarwa ta gidauniyar Kawar Da Shara.

Ta kuma ba da shawar cewa za a iya shirya kwasa-kwasai na koyon sana’a a ƙarƙashin Gidan Afirka domin tallafa wa inganta sana’ar hannu.

Da take magana game da batun shan miyagun ƙwayoyi a ƙasarta, Nguema ta bayyana yadda take neman taimako daga Turkiyya a wannan ɓangaren.

“Na gana da Misis Zita Oligui Nguema, matar shugaban Gabon mai daraja, a Gidan Turkiyya. Ganawarmu ta yi fa’ida, inda ta mayar da hankali kan ƙalubale na duniya, musamman batutuwa na muhalli  da kuma ƙarfafa matan Afirka. Na ji daɗin jin cewa Misis Oligui Nguema tana bibiyar shirinmu na Kawar Da Shara kuma ta  himmatu wajen faɗaɗa waɗannan ayyukan a ƙasarta,” kamar yadda Erdogan ta bayyana a shafin X.

“Kullum Turkiyya a shirye take ta ba da iliminta da ƙwarewarta domin makoma mai ɗorewa. Ina fatan haɗin kai tsakanin ƙasashenmu zai taimaka mana barin duniyar da za a iya rayua a cikinta ga masu zuwa a nan gaba,” a cewarta.

Erdogan ta kuma gana da Prindon Sadriu, matar shugaban Kosovo Vjosa Osmani, a Gidan Turkiyya (Turkevi Center).

A wani saƙon da ta wallafa a shafinta na shafin sada zumunta na Turkiyya NSosyal, Erdogan ta ce su biyun sun jadddada muhimmanci haɗin kai kan batutuwa da za su inganta dangantaka tsakanin Turkiyya da Kosovo.

"Fatanmu ne cewa irin wannan tattaunawa na ƙut-da-ƙut za su ƙara ƙarfafa dangantaka tsakanin Turkiyya da Kosovo,” in ji ta.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#