Dollar

41,4149

0.12 %

Euro

48,8965

0.06 %

Gram Gold

5.038,7100

1.11 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Rikicin ya fara ne a ranar Asabar a lokacin da dakarun Sudan People's Liberation SPLM-IO suka kai hari kan sansanin sojojin SSPDF a Burebiey, wani gari da ke kan iyakar Sudan ta Kudu da Habasha a gundumar Nasir da ke Jihar Upper Nile.

Aƙalla mutum 48 sun rasu a wata arangama tsakanin sojoji da ƙungiyoyin 'yan adawa a Sudan ta Kudu

Aƙalla mutum 48 sun rasa rayukansu kuma fiye da 152 sun jikkata a rikicin da ya ɓarke tsakanin sojojin Sudan ta Kudu da dakarun 'yan adawa a wani gari da ke kan iyaka a arewa maso gabashin ƙasar, kamar yadda kafofin watsa labarai na cikin gida suka ruwaito a ranar Lahadi.

Rikicin ya fara ne a ranar Asabar a lokacin da dakarun Sudan People's Liberation Movement-in-Opposition (SPLM-IO) suka kai hari kan sansanin sojojin South Sudan People's Defense Forces (SSPDF) a Burebiey, wani gari da ke kan iyakar Sudan ta Kudu da Habasha a gundumar Nasir da ke Jihar Upper Nile, kamar yadda Gwamna James Koang ya shaida wa gidan rediyon Eye Radio a ƙasar.

Gwamnan ya ce, bisa ga rahotannin da suka samu, fiye da mutane 48 daga cikin dakarun SPLM-IO da mayaƙan White Army da ke goyon bayansu sun rasu, yayin da fiye da 148 suka jikkata. A ɗayan ɓangaren kuma, SSPDF ba su yi asarar rai ba, sai dai sojoji huɗu sun jikkata.

Koang ya yi kira ga zaman lafiya tare da roƙon dakarun 'yan adawa su dakatar da hare-haren da suke kai wa SSPDF.

'Muna nan don zaman lafiya'

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#