Dollar

41,4195

0.12 %

Euro

48,9416

0.15 %

Gram Gold

5.039,7200

1.13 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Ƙasashen uku sun fitar da wata sanarwa ta haɗin gwiwa inda suka ce ba za su amince da ikon kotun ta Majalisar Dinkin Duniya da ke zaune a birnin Hague ba.

Nijar da Mali da Burkina Faso sun sanar da ficewa daga kotun hukunta manyan laifuka ta ICC

Nijar da Mali da Burkina Faso sun yi shelar ficewa daga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC), suna masu bayyana ta a matsayin wadda ‘yan mulkin mallaka ke amfani da ita wajen gallaza wa marasa ƙarfi.

Ƙasashen uku da ake mulkin soji sun fitar da wata sanarwa ta haɗin gwiwa inda suka ce ba za su amince da ikon kotun ta Majalisar Dinkin Duniya da ke zaune a birnin Hague ba.

"Kotun ICC ta tabbatar wa kanta gazawa wajen hukunta laifukan yaƙi da laifukan take haƙƙin bil’adama da laifukan kisan kiyashi da kuma cin zali," in ji shugabannin uku.

Kawo yanzu dai kotun ba ta yi ce komai ba game da matakin da ƙasashen uku suka ɗauka.

Ƙasashe uku masu maƙwabtaka da juna sun zargi ICC da kasancewa “wata manuniya ta wariya a hukunci a faɗin duniya."

Ƙasashen uku dai sun fice daga ƙungiyar raya attalin arziƙin ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) baya sun zarge ta da kasancewa karyar farautar masu mulkin mallaka.

Kazalika ƙasashen Burkina Faso, Mali da Nijar sun ce suna son fitar da "tsare-tsare na cikin gida na tabbatar da zaman lafiya da adalci ".

Ƙasashen uku sun ƙungiayr ƙasashen Sahel mai suna (AES) a taƙaice a lokacin da suka fara samun matsala da ECOWAS .

Kuma suna ƙoƙarin nesanta kansu daga ƙasashen Yamma, musamman ƙasar Faransa wadda ta yi musu mulkin mallaka inda suke ɗasawa da Rasha da ma wasu ƙasashe domin samun taimako na soji.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#