Dollar

41,4544

0.09 %

Euro

48,7839

-0.37 %

Gram Gold

5.023,8500

0.29 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Kwamitin mai mambobi 35 na ɗaya daga cikin manyan kwamitoci da suke yanke hukunci da sa ido kan batun nukiliya tare da amincewa da kasafin kuɗi da tsara manufofin duniya kan makamashin nukiliya.

IAEA: An zaɓi Nijar a kwamitin gudanarwa na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya

Nijar ta zama mamba a kwamitin gudanarwa na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya (IAEA), matakin da ake ganin wata babbar nasara ce ta diflomasiyya ga ƙasar da ke samar da sinadarin yureniyam.

Matsayin ya biyo bayan zaɓen da aka gudanar a ranar Juma’a 19 ga watan Satumba a ƙarshen taron hukumar IAEA karo na 69 a Vienna, kamar yadda kafar watsa labarai ta ActuNiger ta ambato hukumomin ƙasar suna bayyanawa ranar Talata.

Nijar za ta yi wa'adin shekaru biyu daga shekarar 2025 zuwa 2027.

Kwamitin mai mambobi 35 na ɗaya daga cikin manyan kwamitoci da suke yanke hukunci da sa ido kan batun nukiliya tare da amincewa da kasafin kuɗi da tsara manufofin duniya kan makamashin nukiliya.

Kazalika yanzu Nijar za ta bi sahun ƙasashe 34 da suka haɗa da Togo da Portugal da kuma Saudiyya wajen jagorantar shawarwari kan batutuwan da suka shafi taƙaita yaɗuwar gurbatacciyar iska da samar da tsaro da kuma sarrafa shara.

Tawagar Nijar ƙarƙashin jagorancin ministan muhalli na ƙasar Kanar Maizama Abdoulaye, ta samu nasarar gabatar da cancantar kasancewar ƙasar a cikin kwamitin, inda ta jadadda matsayinta na wadda ke samar da sinadarin yureniyam na tsawon lokaci da kuma burinta na yin tasiri a manufofin nukiliyar duniya.

Hakan na faruwa ne watanni da dama bayan darakta janar na hukumar IAEA Rafael Mariano Grossi ya kai ziyara Jamhuriyar Nijar, inda ya gana da firaminista Ali Lamine Zeine da wasu manyan jami’an gwamnati game da haɗa gwiwa tsakanin ƙasar da hukumar kan amfani da fasahar nukiliya a harkokin zaman lafiya.

Jami'ai a Yamai sun yaba bisa amincewar da aka yi da ƙasarsu a harkokin diflomasiyyar yureniyam na duniya.

A matsayinta na mamba a hukumar IAEA tun daga shekarar 1969, a yanzu Nijar ta samu matsayi daga wadda ke fitar da sinadarin yureniyam zuwa ga wacce za ta ba da gudunmawa wajen tsara makomar makamashin nukiliyar duniya.

Kuma da wannan matsayi, ƙasar za ta samu damar amfani da ƙwarewarta da kuma damarmakin ƙulla ƙawance mai muhimmanci ga ƙasashen duniya a yayin da kuma a ɓangare guda take bunƙasa shirinta na makamashin nukiliya.

Haka kuma samun wannan matsayi, zai jaddada yunƙurin Nijar na taka rawar gani sosai a sauyin samar da makamashi a duniya, inda ta sanya kanta ba kawai a matsayin mai samar da albarkatun ƙasa ba, har ma a matsayin babbar mai taka rawa a tsarin dokokin sarrafa makamashin nukiliya na duniya.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#