Dollar

41,4634

0.17 %

Euro

48,7061

-0.53 %

Gram Gold

5.018,5900

0.18 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Harin da aka kai ranar Juma’a 19 ga watan Satumba rahotanni na zargin cewa makiyaya da ‘yan bindigar da ke kusa da garin ne suka kai.

An gano ƙarin gawarwakin 'yan sandan Nijeriya da 'yan bindiga suka kashe a Benue

An gano ƙarin gawarwakin ‘yan sanda waɗanda ake zargi ‘yan bindiga sun kashe a harin kwanton-ɓauna da aka kai musu a ƙaramar hukumar Katsina-Ala ta Jihar Benue da ke tsakiyar ƙasar.

Harin da aka kai ranar Juma’a 19 ga watan Satumba dai rahotanni na zargin cewa makiyaya da ‘yan bindigar da ke kusa da garin ne suka kai.

An kai harin ne kan wata rundunar jami’an tsaro ta haɗaka da ‘yan sa-kai a Jihar Benue da ake kira Anyam Nyor, a lokacin da suka fita aiki kusa da kan iyakar jihar.

Tun da farko, an tabbatar da mutuwar ‘yan sanda uku mutu yayin da aka bayyana cewa ba a san inda saura takwas suke ba.

Sai dai daga bisani rahotanni sun ambato shugaban ƙaramar hukumar Katsina-Ala, Mista Justine Shaku, yana tabbatar da cewa an gano gawarwakin jami’an tsaron da ake neman lamarin da ya sa adadin waɗanda suka mutu a harin ya kai 11.

“An samu ƙarin gawarwakin jami’an tsaro takwas baya ga ukun da ka riga aka samu,” kamar yadda Mista Shaku ya shaida wa manema labarai.

“Suna kan sintiri ne a kan iyaka a lokacin da lamarin ya faru,” in ji shi.

Martanin rundunar ‘yan sanda

Kawo yanzu rundunar ‘yan sandan ƙasar ba ta tabbatar da mutuwar jami’anta ba.

Sai dai kuma sufeto janar na ‘yan sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun, ya yi gargaɗin cewa rundunar ‘yan sandan ƙasar ba za ta lamunci yadda masu neman ta-da-zaune-tsaye ke ci gaba da kashe jami’ansa ba.

 “A baya, na yi gargaɗi game da hare-haren da ake kaiwa kan jami’an ‘yan sanda da ke gudanar da ayyukansu bisa doka,” kamar yadda jaridar This Day ta ambato shi yana cewa.

“Hare-hare kan jami’anmu abubuwa ne da ba za a lamunta ba. Ba ma lamuntar ko wane irin hari kan jami’an ‘yan sanda da ke ayyukansu bisa doka,” in ji Egbetokun wanda ya yi waɗannan kalaman bayan harin da aka yi a Jihar Benue.

“Na yi kira ga jama’a a-kai-a-kai: idan ba ka gamsu da aikin wani ɗan sanda ba, ka kai ƙara ga hukumomin da suka dace,” a cewar shugaban ‘yan sandan.

 

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#