Sport
Dollar
41,4358
0.08 %Euro
48,9958
0 %Gram Gold
4.984,1300
1.65 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa duk wani bashi da za a karɓa a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Tinubu za a karɓe shi cikin gaskiya, ɗorewa, kuma daidai da tsarin bashi na matsakaicin lokaci na Nijeriya da kuma bin ƙa’idojin duniya.
Kakakin Majalisar Wakilai na Nijeriya Dakta Abbas Tajudeen, ya ce majalisar na tare da Shugaba Tinubu ɗari bisa ɗari a shirinsa na karɓar bashi.
Yayin gabatar da jawabin buɗe taro a taron shekara-shekara na 8 na African Network of Parliamentary Budget Offices Conference, Dokta Tajudeen ya bayyana cewa an yi kuskuren fassara matsayar Majalisar a kan batun gwamnati na karɓar bashi a baya-bayan nan.
Kakakin ya bayyana haka ne a yayin wani taro karo na takwas na ofisoshin kasafin kuɗi na majalisun Afirka inda ya bayyana cewa ana yi wa matsayar majalisa mummunar fahimta dangane da batun cin bashi.
A cewarsa, shirin gwamnati na karɓar bashi a yanzu wani yunƙuri ne na farfaɗo da tattalin arziki tare da tallafa wa manyan ayyuka masu muhimmanci.
Comments
No comments Yet
Comment