Sport
Dollar
41,3607
-0.04 %Euro
48,8272
0.38 %Gram Gold
4.983,4600
1.63 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%A jimilla, gwamnatin Nijeriya ƙarƙashin Shugaba Bola Tinubu ta ƙwace lasisin haƙar ma’adinai 3, 794 ciki har da lasisi 619 da aka ƙwace domin gaza biyan haraji na shekara-shekara da kuma 912 da aka ƙwace saboda rashin aiki da su.
Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ƙwace lasisin haƙar ma’adinai 1,263 saboda dalilai na kasa biyan haraji na shekara-shekara.
Ministan Ma’aikatar Ci-gaban Harkar Ma’adinai Dele Alake ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da mai magana da yawunsa Segun Tomori, ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
Sanarwar ta ce cikin lasisi da gwamnatin ta ƙwace akwai lasisi 584 na bincike da lasisi 65 na haƙar ma’adinai da lasisi 144 na kwasar duwatsu da kuma lasisi 470 na ƙananan masu haƙar ma’adinai.
Comments
No comments Yet
Comment