Dollar

41,3612

-0.04 %

Euro

48,8532

0.43 %

Gram Gold

4.979,0700

1.54 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Kocin tawagar ƙwallon ƙafa ta Masar, Hossam Hassan ya ce lokaci ya yi da ƙwallo za ta yi wa Mohamed Salah adalci tahanyar ba wa bamisiren kyautar Ballon d'Or ta bana.

Kocin Masar ya nemi a bai wa Salah kyautar Ballon d'Or ta bana

Yayin da awanni ne suka rage a ayyana wanda ya zama gwarzon ƙwallo ƙafa na duniya a bana, kocin tawagar ƙasar Masar, Hossam Hassan ya yi kira da a girmama tauraron ƙwallo na ƙasar, Mohamed Salah.

Salah na cikin jerin taurarin ‘yan ƙwallon da za a zaɓa don fitar da wanda zai lashe kyautar Ballon d'Or ta shekarar 2025.

Da yake ayyana Salah a matsayin ‘gwarzo abin koyi, Hassan ya ce ɗan wasan da ke buga wa Liverpool ta Ingila, abin koyi ne ga masu neman nasara a fannin ƙwallo a duniya.

A kakar bara, Mohamed Salah dai ya ciyo wa Liverpool ƙwallaye 34 a duka gasanni kuma ya taka rawar gani wajen taimaka wa ƙungiyarsa lashe kofin Firimiya.

Da wuya Salah ya kai labari

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#