Sport
Dollar
41,2811
0.1 %Euro
48,8666
-0.28 %Gram Gold
4.860,2200
-0.66 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Tauraron ɗan wasan Real Madrid, Kylian Mbappe ba zai halarci bikin ba da kyautar Ballon d'Or ba, kuma ya sanar da zaɓinsa na wanda ya kamata ya lashe kyautar.
A karo na biyu a jere, tawagar Real Madrid ta Sifaniya za ta ƙaurace wa bikin ba da kyautar gwarzon ɗan ƙwallon ƙafa na duniya na bana, wanda za a yi ranar 22 ga Satumba.
Shi ma tauraron ɗan wasan Real Madrid, Kylian Mbappe ya tabbatar da cewa ba zai halarci bikin da za a yi a babban birnin ƙasarsa na Paris ba.
Maimakon haka, ɗan wasan ya sanar da cewa zai kalli bikin a gida a talabijin.
A kakar bara, haziƙin ɗan wasan ɗan asalin Faransa ya ci ƙwallaye 44 a duka gasanni, inda ya zama wanda ya fi kowa cin ƙwallo a gasar La Liga.
Sai dai duk da gwanintar da ya nuna a kakarsa ta farko a Madrid, Mbappe ba ya tunanin yana da nasibin lashe Ballon d'Or, saboda Real Madrid ba ta lashe wani babban kofi a kakar ba.
Mbappe ya sanar da wannan ne a tattaunawarsa da ‘yan jarida bayan wasan Real Madrid da Marseille a gasar Zakarun Turai a Santiago Bernabeu ranar Talata.
Waye zaɓin Mbappe?
Comments
No comments Yet
Comment