Dollar

41,2910

0.2 %

Euro

48,4340

0.61 %

Gram Gold

4.758,6800

1.43 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Tsohon ɗan wasan Real Madrid da Manchester City, kuma tsohon ɗan tawagar ƙwallon Brazil ya gaza yin nasara a ƙarar da ya ɗaukaka a kotun ƙoli kan hukuncin shekara tara da aka masa kan laifin fyaɗe.

Robinho: Tsohon ɗan wasan Real Madrid da Milan zai yi zaman yarin shekara 9 a Brazil

Kotun Ƙolin Brazil ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar da tsohon ɗan ƙwallon tawagar ƙasar, Robinho ya yi game da hukuncin shekaru tara da aka yanke masa kan zargin aikata fyaɗe.

Mai shekaru 41, Robinho tsohon ɗan wasan ƙungiyoyin Turai ne daban-daban kamar Real Madrid, AC Milan, Manchester City, da kuma Santos ta Brazil.

Tun a 2017 ne kotu ta kama shi da zama cikin gungun mazan da suka yi wa wata mata ‘yar Albania da ke bikin cika shekar 23 a wani gidan rawa na birnin Milan fyaɗe a 2013.

Laifin ya faru ne lokacin Robinho yana buga wa AC Milan ta Italiya wasa, kuma kotun Italiya ta tabbatar da hukuncin a Janairun 2022.

Ana tsare da Robinho a gidan yarin Tremembe da ke nisan kilomita 150 daga babban birnin Brazil, wato Sao Paulo tun a Maris ɗin 2024.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#