Sport
Dollar
41,2861
0.06 %Euro
48,4058
0.05 %Gram Gold
4.770,3200
0.31 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Leverkusen ta sallami kocinta Erik Ten Hag bayan jagorantar wasa biyu kacal a kakar Bundesliga ta bana, da ƙarin wasa guda kafin nan.
Bayer Leverkusen ta Jamus ta kori sabon kocinta Erik ten Hag sakamakon rashin nuna tagomashi a aikinsa.
Leverkusen ta sanar a hukumance cewa ta sallami Erik Ten Hag bayan wani mataki da shugabancinnin ƙungiyar suka zartar ranar Alhamis da ta gabata.
Ten Hag wanda ɗan asalin Netherlands ne ya samu wannan labari a sirrance yayin wani taro da shi a safiyar Litinin.
Tsohon kocin Manchester United da Ajax, Ten Hag ya je Leverkusen ne a Mayun da ya gabata, kuma ya jagorance su buga jimillar wasanni uku kacal tun bayan zuwansa.
A kakar Bundesliga ta bana, kocin ya jagoranci buga wasanni biyu ne kawai, inda aka doke su a na farko, sannan suka yi canjaras a na biyu.
Comments
No comments Yet
Comment