Dollar

41,2664

0.06 %

Euro

48,4397

0.18 %

Gram Gold

4.771,8900

0.34 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

An kai harin ne ranar Juma’a da daddare a garin Darul Jamal, wanda ke da sansanin soji a kan iyakar Nijeriya da Kamaru.

Dar-El-Jamal: ‘Yan Boko Haram sun kashe mutum 63 a Jihar Borno a Nijeriya

’Yan ta’adda na Boko Haram sun kashe aƙalla mutum 63  a wani gari na arewa maso gabashin Nijeriya yayin da suka far ma garin da aka mayar da mutanensa daga sansanin ‘yan gudun hijira, in ji gwamnan jihar.

An kai harin ne ranar Juma’a da daddare a garin Darul Jamal, wanda ke da sansanin soji a kan iyakar Nijeriya da Kamaru.
Babagana Zulum, gwamnan Jihar Borno da ke fuskantar ƙalubalen tsaro, ya ce sojoji biyar na cikin waɗanda suka mutu, adadin da wata majiyar tsaro ta tabbatar wa kamfanin dillancin labaran AFP.
"Abin takaici ne, an sake tsugunar da wannan al’ummar ne cikin watannin da suka wuce kuma sun ci gaba da lamuransu na yau da kullum," kamar yadda Zulum ya sanar da ‘yan jarida a wurin da aka kai harin.


'Ihu da harbin kan mai-uwa-da-wabi'
"Kawo yanzu, mun tabbatar da rasuwar mutum 63, ciki har da fararen-hula da sojoji."

Mazauna garin sun ce an fara harin ne da misalin ƙarfe 8:30 na dare (ƙarfe 7:30 agogon GMT), lokacin da gomman mayaƙa suka iso bisa babura suna harbi da kuma ƙona gidaje.
"Sun zo suna ihu kuma suna harbin kan mai-uwa-da-wabi," kamar yadda Malam Bukar, wanda ya tsere da matarsa da ‘ya’ya uku ya shaida wa AFP.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#