Sport
Dollar
41,3687
0.09 %Euro
48,5985
-0.05 %Gram Gold
4.849,6400
0.44 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Tsohon golan Manchester United, Andre Onana ya ce bai taɓa ganin soyayyar da ya gani a ƙungiyar Trabzonspor ta Turkiyya ba, inda ya koma aro a makon nan.
Andre Onana, tsohon golan Manchester United ya ce bai taɓa ganin soyayyar da ya gani a ƙungiyar Trabzonspor ta Turkiyya ba, inda ya koma aro a makon nan.
Onana ya kammala komawa Trabzonspor aro bayan da aka tilasta masa barin Man U, inda aka rage masa daraja a zaɓar masu buga wasa ƙarƙashin koci Ruben Amorim.
Ɗan asalin Kamaru, Onana ya je United ne a 2023 kan kuɗi fam miliyan 47.2.
A yanzu zai nemi farfaɗo da tagomashinsa a gasar Super Lig ta Turkiyya, inda ya bayyana tsananin farin cikinsa da yadda ya samu tarba a Turkiyya.
A maraicen Alhamis ne Manchester United ta tabbatar da ƙaurar Onana mai shekaru 29 zuwa Trabzonspor a matsayin aro na tsawon kakar 2025-26.
Kocin United ya zaɓi yin aiki tare da golansa na biyu Altay Bayindir, kafin daga bisani ya sayo wani golan, Lammens kan fam miliyan 18.2.
Kurarin Onana
Comments
No comments Yet
Comment