Dollar

42,3199

-0.01 %

Euro

49,2354

-0.28 %

Gram Gold

5.559,7500

-1.71 %

Quarter Gold

9.406,9400

-3.17 %

Silver

69,0600

-2.84 %

Taron ƙaddamar bikin wanda aka gudanar a Cibiyar Al'adu ta Atatürk da ke Istanbul ya hada kan manyan masana, masu fasaha, fitattun mutane a fannin al'adu da ɓangaren matasa.

Shugaba Erdogan ya ƙaddamar da baje-kolin 'Echoes' domin tunawa da Sule Yuksel Senler and Malcolm X

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da Uwargidansa Emine Erdogan sun ƙaddamar da bikin baje-kolin Echoes a ranar Jumma'a, inda ake murnar wanda ke murnar tarih mai ɗorewa da Sule Yuksel Senler da Malcolm X suka bari— mutane biyu masu karfi wadanda suka tsara muhawarar duniya kan adalci, hakki da mutuncin ɗan’adam.

Taron ƙaddamar bikin wanda aka gudanar a Cibiyar Al'adu ta Atatürk da ke Istanbul ya hada kan manyan masana, masu fasaha, fitattun mutane a fannin al'adu da ɓangaren matasa.

Daga cikin bakin da suka halarta akwai 'yar Malcolm X, Ilyasah Shabazz, Uwargidan Shugaban Senega Marie Khome Faye, da Mataimakiyar Shugabar Jam’iyyar AK Majalisa wadda kuma ita ce Shugabar Hukumar Amintattun Gidauniyar Sule Yuksel Senler, Leyla Sahin Usta.

Za a gudanar da bikin har zuwa 27 ga Nuwamba, kuma shi ne wani bangare na Taron Duniya kan Hakkin Dan Adam kuma ana gayyatar mutane domin su yi ga tarin hotuna waɗanda aka ajiye na tarihi, takardu, da rikodin na sauti da bidiyo.

Yaki don hakki da 'yanci

Shugaba Erdogan ya ce yana farin ciki da haduwa da al'ummar masana, al'adu da masu fasaha na Turkiyya, yana mai jaddada muhimmancin kiyaye mutunci da na waɗanda ke fafutuka don hakki da 'yanci a tsawon zamani.

“Wannan muhimmnin baje-kolin na wakiltar wasu tarihi na fafutuka na tsawon lokaci don adalci da daraja, wanda yanzu yake yawo a zuciyar Istanbul,” in ji shi.

Masu shirya taron sun lura cewa "Yankılar (Echoes)" na haskaka tasirin da ba ya gushewa na Sule Yuksel Senler — marubuciya ce ta Turkiyya wacce ta jagoranci fafutukar hakkin ɗan’adam — da Malcolm X, jagoran gwagwarmayar hakkin farar-hula wanda ake girmamawa a duniya, kuma gadon da ya bari na ci gaba da zuga gwagwarmayar neman 'yanci daga Amurka zuwa Afirka da duniyar Musulunci.

An gode wa Gidauniyar Sule Yuksel Senler da Cibiyar Dr. Betty Shabazz, tare da sauran masu bada gudunmawa da dama, saboda kokarinsu na ganin wannan baje-kolin ya tabbata.

Jami'ai sun bayyana fatan cewa baje-kolin zai ƙarfafa wayar da kan duniya game da hakki, adalci da mutuncin ɗan’adam, kuma ya zama tushen abin da zai ƙarfafa gwiwar matasa a Turkiyya da wajen ta.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#