Sport
Dollar
43,3989
0.09 %Euro
51,5670
0 %Gram Gold
7.071,9600
0.37 %Quarter Gold
11.912,4400
0 %Silver
150,8800
-0.26 %An yi zargin an ɓoye ƙwayoyin da darajarsu ta kai Naira biliyan uku a wasu kunshin mazubin gahawa inda aka kama su a filin jiragen saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja.
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) ta kama wata ’yar kasar Brazil mai shekaru 30 Imgrid Benevides, dauke da kilogram 30.09 na hodar iblis.
A wata sanarwa a ranar Lahadi, kakakin NDLEA Femi Babafemi ya ce an ƙunshe miyagun ƙwayoyin a mazubin gahawa ’yar kamfani inda aka kama su a filin jiragen saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja.
Ya ce an kama wacce ake zargin a ranar Jumma’a bayan ta iso Abuja a jirgin saman Qatar Airways.
Hukumar ta ce Benevides, jami’ar tsaro ta musamman ce a Brazil da aka sanya idanu a kan motsin ta kafin a kama ta a filin jirgin saman Abuja.
“A lokacin da aka bude kunshin gahawa din, maimakon a ga gahawa da ake sha, sai aka ga wasu fararen abubuwa wadanda bayan an yi gwaji aka tabbatar da hodar iblis ce mai nauyin kilogram 30.09, wanda shi ne kamen hodar iblis mafi girma da aka taba yi a lokaci guda,” in ji sanarwar.
A binciken da aka gudanar, matar ta ce ta sayo miyagun kwayoyin ne da niyyar zuwa Nijeriya hutu.”
Kazalika, a Filin Jiragen Sama na Murtala Mohammed NDLEA an kama Adediran Adedoyin da Afatakpa Ochuko a ranar 20 ga Janairu a yayin da suke shirin tafiya Istanbul, Turkiyya.
Ya ce an kama wadanda ake zarfin da kwayoyi 3,990 na tapentadol da tramadol da aka boye a cikin kayan abinci da ke cikin jakankunansu.
Sanarwar ta ci gaba da cewa jami’an NDLEA a teku sun kama wani jirgin ruwa a gabar Lekki dauke da manyan jakankuna 44 cike da tabar wiwi da aka dauko daga Ghana. Tabar wiwin na da nauyin kilogtam 1,848 a ranar 22 ga Janairu.
Babafemi ya kuma a ce a Kaduna ma an kama Aminu Baba mai shekara 20 da Abdulrashid Abubakar mai shekara 28 dauke da wasu jakankuna da ke dauke da abubuwan fashewa guda 140 a kan hanyar Zaria-Kaduna.
Ya ce an ƙwace abubuwan fashewar tare da kama mutanen a yayin binciken ababen hawa da ake gudanarwa.
Comments
No comments Yet
Comment