Sport
Dollar
43,4071
0.01 %Euro
51,4937
0.3 %Gram Gold
6.946,1400
0.01 %Quarter Gold
11.584,3300
0 %Silver
142,9800
0.01 %Tinubu zai kai ziyarar ce domin “ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu tare da faɗaɗa haɗin kai a fannin tsaro, ilimi, ci gaban walwala, ƙirƙire-ƙirƙire da sufurin jiragen sama.”
Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu zai tashi daga Abuja ranar Litinin, 26 ga watan Janairun 2026 zuwa Ankara, babban birnin Turkiyya inda zai kai ziyarar aiki a ƙasar.
Wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai magana da yawun shugaba ƙasar Nijeriya ya fitar ranar Lahadi ta ce Tinubu zai kai ziyarar ce domin “ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu tare da faɗaɗa haɗin kai a fannin tsaro, ilimi, ci gaban walwala, ƙirƙire-ƙirƙire da sufurin jiragen sama.”
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya kai ziyarar aiki Nijeriya daga 19 zuwa 20 ga watan Okotoban 2021, in ji sanarwar.
Ta ƙara da cewa yayin ziyarar ta Shugaba Tinubu, ƙasashen biyu za su tattauna kan harkokin siyasa da na diflomasiyya da kuɗi da sadarwa da cinikayya da kuma zuba jari.
Kazalika yayin ziyarar, manyan jami’ai da ‘yan kasuwa na ƙasashen biyu za su gana tare da sanya hannu kan yarjeniyoyi game da binciken kimiyya, makamashi, haɗin kai a fannin fasaha, harkokin watsa labarai da sadarwa, haɗin kai a fannin soji da sauransu.
Manyan jami’an da ke cikin tawagar Shugaba Tinubu sun haɗa da Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tuggar; Ministan Shari’a kuma Antoni Janar, Prince Lateef Fagbemi SAN; Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (ritaya) da shugaban kwamitin tsaro na majalisar wakilan Nijeriya, Honorabul Jimi Benson.
Sauran sun haɗa da: Ministar Harkokin Mata, Hajiya Imaan Suleiman-Ibrahim; Ministan Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo; Ministar Al’adu da Tattalin Arzikin Fasaha, Hannatu Musawa; Mai Bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaro, Malam Nuhu Ribadu; da darakta janar na hukumar Leƙen Asiri ta Nijeriya, Ambasada Mohammed Mohammed.
Comments
No comments Yet
Comment