Dollar

43,4109

0.07 %

Euro

51,5609

0.44 %

Gram Gold

7.015,9600

1.01 %

Quarter Gold

11.584,3300

0 %

Silver

146,4800

2.46 %

Rundunar Sojin Nijeriya ta karyata rahoton cewa Ibrahim Nazifi ya mutu yayin horaswa a Depot Zariya, tana mai cewa bai taɓa halartar horaswar ba.

Rundunar Sojin Nijeriya ta ƙaryata wani rahoto na zargin mutuwar kurtu a Depot na Zaria

Rundunar Sojin Nijeriya ta ƙaryata rahotannin kafafen yaɗa labarai da ke cewa wani ɗan asalin Jihar Gombe mai suna Ibrahim Nazifi ya rasu yayin atisayen horaswa a sansanin horas da kuratan sojoji na Depot da ke Zariya, inda ta bayyana rahotannin a matsayin ƙarya da ruɗani.

A cikin wata sanarwa da Depot ɗin ta fitar ta bayyana cewa bayanan da suke da su sun nuna cewa Nazifi, mai lambar neman shiga aiki 90RRI-GO-9017726, ya yi nasarar tsallake tantancewar ɗaukar soji wadda aka gudanar a watan Disamban 2025, sannan aka zaɓe shi don halartar horaswa a Depot ɗin Zariya. Sai dai rundunar ta ce bai taɓa zuwa wajen horaswar ba kuma ba a taɓa karɓarsa cikin shirin ba.

Sanarwar ta ce, “Ibrahim Nazifi bai taɓa kasancewa a Depot na Rundunar Sojin Nijeriya da ke Zariya ba, kuma bai taɓa shiga kowanne irin atisayen horaswa ba. Saboda haka, Depot ɗin ba ta da wani bayani na jin rauni ko mutuwarsa yayin horaswa.”

Rundunar Sojin ta buƙaci Gwamnatin Jihar Gombe da sauran hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da cikakken bincike domin gano a ina, yaushe da kuma a wane yanayi aka ce mutuwar ta faru, tana mai jaddada cewa babu lamari irin wannan da ya faru a cikin Depot ɗin Zariya.

Rundunar ta kuma ce tana sane da cewa atisayen soji na da wahala ta fuskar jiki kuma an tsara shi ne don samar da juriyar jiki, jajircewa da shirye-shiryen yaƙi, Rundunar Sojin Nijeriya ta nuna cewa akwai tsauraran matakan tsaro, kulawar lafiya da hanyoyin rage haɗari domin kare masu horaswa da rage yiwuwar samun rauni.

Depot ɗin ta Zariya ta kuma yi gargaɗi ga jama’a da su guji yaɗa bayanan da ba a tantance ba, tana mai cewa irin waɗannan rahotanni na iya ruɗar da al’umma tare da cutar da martabar Rundunar Sojin Nijeriya ba tare da dalili ba.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#