Sport
Dollar
43,3762
0.27 %Euro
51,0198
0.18 %Gram Gold
6.919,9800
1.2 %Quarter Gold
11.455,2500
2.32 %Silver
139,8000
4.55 %Wata sanarwa ta ce Poroy yana fatan za a iya sanya hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa tsakanin Turkiyya da Nijeriya a lokacin ziyarar da Shugaba Bola Tinubu zai kai Turkiyya.
Turkiyya ta gano kayayyakin tarihi guda 76 na katako da ƙarafa da ake kyautata zaton mallakin Nijeriya ne, wanda hakan ke share fagen mayar da su gida da kuma ƙarfafa alaƙar al'adu tsakanin ƙasashen biyu, in ji jakadan Turkiyya a Nijeriya, Mehmet Poroy.
Jakadan, wanda ya yi magana a ranar Alhamis lokacin da ya ziyarci Ministar Fasaha, Al'adu, Yawon Bude Ido da Tattalin Arzikin Kirkire-kirkire ta Nijeriya, Hannatu Musa Musawa, a Abuja, ya ce tattaunawa kan dawo da su za ta fara ne lokacin da Nijeriya ta gane su kuma ta ce natan ne.
Wata sanarwa ta ce Poroy yana fatan za a iya sanya hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa tsakanin Turkiyya da Nijeriya a lokacin ziyarar da Shugaba Bola Tinubu zai kai Turkiyya.
"Ministanmu na Al'adu da Yawon Buɗe ido ya gano abubuwa 76 na katako da ƙarfe waɗanda suke ganin na Nijeriya ne. Mun sami bayanai game da waɗannan kayan tarihi a watan Mayun da ya gabata kuma muna son a dawo da su.
"Muna fatan sanya hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa a lokacin ziyarar Shugaban Nijeriya zuwa Turkiyya. Za mu inganta fahimtar al'adu da haɗin gwiwa a tsakaninmu," in ji shi.
Ambasada Poroy ya tattauna kan shirye-shiryen kafa cibiyar al'adu a Nijeriya don bunkasa fasahar gargajiya da kuma ilmantar da matasan Nijeriya.
Hannatu Musawa ta lura da muhimmancin kammala yarjejeniyar, tana mai kira ga jami'ai da su hanzarta aiwatar da wannan tsari.
Ministar ta nuna sha'awar Nijeriya ta hada kai da Turkiyya kan ayyukan masana'antar fina-finai, musayar al'adu, da kuma karfafa mata a fannin ado.
Ta jaddada rawar da Nijeriya ke takawa a tattaunawar al'adu ta duniya, musamman a yankin Kudu maso Gabashin Duniya, da kuma yiwuwar hadin gwiwar Turkiyya da Najeriya don inganta fahimtar al'adu da ci gaban tattalin arziki.
Comments
No comments Yet
Comment