Dollar

43,3769

0.27 %

Euro

51,0255

0.19 %

Gram Gold

6.917,7000

1.17 %

Quarter Gold

11.455,2500

2.32 %

Silver

139,5000

4.32 %

Manoman da barnar ta shafa sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) cewa dabbobin sun fito ne daga wani kogi da ke kusa kana suka lalata amfanin gona da suke gab da girbinsu.

Dorinar ruwa sun lalata gonaki da dama a Jihar Gombe, manoma sun tafka manyan asara

Akalla gonaki 17 da suka kai kimanin hekta 14 ne wasu dorinar ruwa suka mamaye a daren ranar Talata a ƙauyen Hinna na yankin karamar Hukumar Yamaltu/Deba ta jihar Gombe.

Manoman da abin ya shafa sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) cewa dabbobin sun fito ne daga wani kogi da ke kusa kana suka lalata amfanin gona da suka kusa girbinsu, lamarin da ya yi wa rayuwarsu mummunar illa kuma yake barazana ga tsaron abinci na yankin.

Shugaban manoma na yankin, Zakari Ladan, ya bayyana hare-haren da dorinar ruwan ke yawan kai wa yankin a matsayin abin takaici, yana mai cewa manoma sun sha wahala tsawon shekaru ba tare da gwamnati ta kawo musu ɗauki ba.

Kazalika, ya kiyasta asarar da aka yi ta kusan Naira miliyan bakwai, yana mai bayyana cewa an lalata amfanin gona kamar na masara da shinkafa da tumatir da barkono da kuɓewa da karas da kuma kankana.

Ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa, manomin masara Mohammed Zengina, ya ce ya yi asarar fiye da hekta 1.5 na amfanin gona wanda darajarsu ta kai kimanin ₦800,000 a cikin dare ɗaya, ya ƙara da cewa har yanzu bai farfaɗo daga makamancin irin wannan abu da suka faru a baya ba.

Kazalika, su ma manoman shinkafa a yankin sun koka game da wannan barna, duk kuma da tara kuɗin da suka yi don biyan mafarauta su yi musu gadin gonakinsu.

Da yake mayar da martani kan lamarin, Kwamishinan Noma na Jihar Gombe, Dakta Barnabas Malle, ya tabbatar da cewa gwamnati ta ssamu labarin harin da dabbobin suka kai.

Ya ce, an tura jami'ai don tantance yawan barnar kuma za su gabatar da rahoto ga Gwamna Inuwa Yahaya don neman diyya ko kuma taimakon gaggawa.

Kwamishinan ya yi kira ga manoman da abin ya shafa da su ƙara haƙuri, inda ya tabbatar musu da cewa gwamnatin jihar na ɗaukar matakai don magance lamarin.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#