Sport
Dollar
0,0000
%Euro
0,0000
%Gram Gold
0,0000
%Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Shirin ya ƙunshi daukar nauyin Aikin Hajji da Umrah da ba shi sabon gida, da kuma cikakken tallafin walwala.
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da wani cikakken shirin jin dadin rayuwa da walwala ga uban yara shida da matarsa da aka yi wa kisan gilla a yankin Chiranci Dorayi na jihar Kano.
Shirin ya ƙunshi daukar nauyin Aikin Hajji da Umrah da ba shi sabon gida, da kuma cikakken tallafin walwala.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu a ranar Alhamis.
Gwamna Yusuf ya sanar da wannan shirin ne a lokacin ziyarar ta'aziyya da ya kai ga iyalan mamatan, inda ya nuna matukar tausayawa tare da tabbatar musu da jajircewar gwamnatin jihar na tallafa wa mahaifin wajen sake gina rayuwarsa.
Ya ba da umarnin a samar masa da gida mai kyau, sannan ya yi alƙawarin tallafin gwamnati don ba shi damar sake yin aure da kuma sake zama cikin jama'a.
Dangane da batun adalci, gwamnan ya umarci Babban Lauyan Jihar Kano da Kwamishinan Shari'a da su gaggauta gurfanar da wadanda ake zargi da hannu a kisan. Ya tabbatar da cewa duk wadanda aka samu da laifi za su fuskanci cikakken hukunci a kan lamarin.
Gwamna Yusuf ya ci gaba da bayyana cewa zai sanya hannu kan zartar da hukuncin kisa ga duk wani mai laifi da aka samu da hannu a kisan na Chiranci Dorayi, yana mai cewa wannan matakin zai kuma shafi wadanda suka kashe Hanifa da wanda ya ƙona masallata a Gezawa, da zarar kotuna sun yanke musu hukuncin da ya dace.
Ya yaba wa rundunar 'yan sandan Nijeriya da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), da sauran hukumomin tsaro saboda kokarinsu na gaggawa da kuma hadin gwiwa wanda ya kai ga kama wadanda ake zargin.
Domin nuna godiya ga abin da gwamnati ta yi, magidancin ya ce ya bayar da gidansa na kansa ga Gwamnatin Jihar Kano don gina makarantar Islamiyya don yi wa al'umma hidima.
Comments
No comments Yet
Comment