Dollar

0,0000

%

Euro

0,0000

%

Gram Gold

0,0000

%

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Wadda ake zargin ta shaida wa 'yansanda cewa auren dolen da iyayenta suka yi mata ne ya sa ta saka wa mijin nata maganin ɓera a abincinsa.

‘Yansandan Nijeriya sun kama wata sabuwar amarya a Jigawa kan zargin kashe angonta da maganin ɓera

 Rundunar ‘Yansandan Nijeriya reshen Jihar Jigawa ta kama wata sabuwar amarya bisa zargin saka guba wadda ta kai ga mutuwar mijinta a ƙauyen Gauza da ke Ƙaramar Hukumar Jahun.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:00 na yammacin ranar 23 ga Janairun 2026, inda marigayin ya ci abincin rana da matarsa ta shirya masa a gida, bayan haka ya kamu da mummunar rashin lafiya. An gaggauta kai shi asibiti domin samun kulawar likita, sai dai an tabbatar da rasuwarsa yayin da ake masa magani.

‘Yansandan sun ce an aika jami’ai nan take inda suka je suka kamo sabuwar amaryar wadda ita ake zargi.

A yayin da ake mata tambayoyi, amaryar ta bayyana cewa ta saka maganin ɓera a cikin abincin mijin nata, kamar yadda sanarwar ‘yansandan ta tabbatar. Ta kuma bayyana cewa ta aiki ɗanuwanta ne domin sayo maganin ɓeran wanda ta yi amfani da shi wurin aikata laifin.

Wadda ake zargin ta shaida wa masu gudanar da binciken cewa iyayenta sun yi mata auren dole ne, wanda lamarin ne ya kai ta ga aikata wannan aikin.

Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar ya bayar da umarnin mika lamarin zuwa ga Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jiha (SCID) da ke Dutse domin zurfafa bincike. Rundunar ta ce za a gurfanar da wadda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

Rundunar  ‘yansandan ta bukaci al’umma da su zauna lafiya, su bi doka, tare da neman hanyoyin shari’a wajen warware matsalolin iyali da na aure. Ta kuma gargadi jama’a da kada su ɗauki doka a hannunsu, domin irin waɗannan matakai kan haifar da sakamakon da ba za a iya mayar da hannun agogo baya ba.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#