Dollar

43,4084

0.09 %

Euro

51,6919

0.22 %

Gram Gold

7.065,1300

0.27 %

Quarter Gold

11.912,4400

0 %

Silver

153,0000

1.14 %

Abba Kabir ya shiga jam'iyyar ne bayan da aka shafe makonni ana dakon shigar tasa, lamarin da ya sa fagen siyasar Jihar Kano ya ɗauki ɗumi, musamman bayan fahimtar ɓaraka tsakaninsa da ubangidansa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya shiga Jam'iyyar APC

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf a hukumance ya koma Jam’iyyar APC.

Ya koma jam’iyyar ne a yayin wani taron karɓarsa cikin jam’iyyar da aka gudanar a ranar Litinin a babban ɗakin taron gidan gwamnatin Kano.

 A wasu bidiyoyi da suka yaɗu a shafukan sada zumunta, an ga gwamnan tare da wasu jiga-jigan APC na Kano da suka haɗa da mataimakin shugaban majalisar dattijai, Sanata Barau Jibrin, da tsohon gwamnan jihar Abdullahi Ganduje, da Sanata Kawu Sumaila da A.A Zaura da Abdullahi Abbas, shugaban APC na Kano da sauransu.

Abba Kabir ya shiga jam'iyyar ne bayan da aka shafe makonni ana dakon shigar tasa, lamarin da ya sa fagen siyasar Jihar Kano ya ɗauki ɗumi, musamman bayan fahimtar ɓaraka tsakaninsa da ubangidansa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.

A yayin jawabinsa, Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa za su ƙara zage damtse domin gudanar da ayyuka sannan ya jaddada cewa gwamnatinsa ta matasa ce inda ya ce za a ci gaba da tafiya da matasa a cikin gwamnatinsa.

Haka kuma gwamnan ya jaddada cewa jama’a za su ga canji a Kano da da haɗin kan da ba a taɓa gani ba.

A nasa jawabin, tsohon gwamnan Kano kuma tsohon shugaban Jam’iyyar APC Abdullahi Umar Ganduje ya yi wa Abba Kabir maraba da shiga APC sannan ya tabbatar da cewa a halin Abban shi ne jagoran APC a Jihar Kano.

Hakazalika Sanata Barau Jibril mai wakiltar Kano ta Kudu shi ma ya yi wa Abba maraba sannan ya buƙaci duk wani mai goyon bayansa, lallai ya goyi bayan Abba Kabir Yusuf.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#