Sport
Dollar
43,4018
0.1 %Euro
51,5993
0.03 %Gram Gold
7.087,9200
0.59 %Quarter Gold
11.912,4400
0 %Silver
153,2400
1.3 %Sojojin Sudan sun sha alwashin ci gaba da yaƙi da dakarun RSF har sai sun maido da zaman lafiya a faɗin ƙasar.
Rundunar sojin Sudan ta ce dakarunta sun karya ƙawanyar da mayaƙan RSF suka kwashe fiye da shekara ɗaya da rabi suna yi wa birnin Dilling da ke kudancin ƙasar, inda suka hana shiga cikinsa.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, rundunar ta ce dakarunta sun yi “nasarar buɗe hanyar zuwa Dilling bayan sun ƙaddamar da gagarumin harin soji," tana mai cewa dakarun nata sun yi "mummunar ɓarna" ga mayaƙan Rapid Support Forces (RSF).
Sojojin Sudan sun sha alwashin ci gaba da yaƙi da dakarun RSF har sai sun maido da zaman lafiya a faɗin ƙasar.
Idan wannan iƙirari ya tabbata, rundunar sojin za ta ƙara ƙarfi a yankin arewaci da na kudanci da ke kan hanyar zuwa birnin Dilling, wanda ke jihar Kudancin Kordofan.
Birnin yana tsakiyar hanyar zuwa Kadugli — babban birnin da aka yi wa ƙawanya — da kuma El‑Obeid, babban birnin jihar Arewacin Kordofan, wanda dakarun RSF suka nemi yi wa ƙawanya.
Wasu bidiyoyi da aka watsa a shafukan sada zumunta sun nuna sojojin Sudan a cikin Dilling, inda suke ta murna a cikin manyan motocin a-kori-kura sannan mutane suna jinjina musu.
Gagarumin farmaki
Gagarumin faramakin da sojojin suka kai a Dilling da kewayensa na zuwa ne a yayin da suke yunƙurin hana dakarun RSF ci gaba da kutsawa zuwa yankin Kordofan.
Tun bayan da mayaƙan RSF suka ƙwace babbar tungar sojoji a yammacin Darfur a watan Oktoban da ya gabata, sun mayar da hankali zuwa gabashi, inda suke samun goyon baya daga mayaƙan wani ɓangare na Sudan People's Liberation Movement waɗanda Abdelaziz al-Hilu yake jagoranta.
Kuma tun daga wancan lokaci, mayaƙan na RSF sun matsa ƙaimi wajen kai hare-hare a Yammacin Kordofan, inda suka ƙwace garin Heglig — wanda ke da rijiyoyin man fetur mafi girma a Sudan — tare da ƙara himma wajen yi wa Kadugli ƙawanya.
Comments
No comments Yet
Comment