Dollar

43,3981

0.1 %

Euro

51,5153

-0.08 %

Gram Gold

7.096,0800

0.71 %

Quarter Gold

11.912,4400

0 %

Silver

157,3200

4 %

Shugaban sojin Sudan ya ce tattaunawar da ta haɗa RSF na jinkirta rikici ne kawai

Burhan: Ba Zaman Lafiya a Sudan Sai an Kawar da RSF

Shugaban gwamnatin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, ya ce ba za a taɓa samun zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasar ba sai an kawar da rundunar Rapid Support Forces (RSF), yana mai cewa duk wata tattaunawar zaman lafiya da aka haɗa RSF a cikinta na ƙara jinkirta rikicin ne kawai. Ya bayyana hakan ne yayin ganawa da ‘yan jarida a Port Sudan. (TRT Hausa)

Burhan ya ce kawar da RSF ba yana nufin kashe dukkan dakarunta ba ne, illa dai ya na nufin su miƙa makamansu su yi saranda, yana mai jaddada cewa yaƙin da ake yi ya haddasa gagarumar ɓarna ga fararen-hula da gine-gine a faɗin ƙasar. (TRT Hausa)

Ya ƙara da cewa duk da irin wahalar da yaƙin ya jefa al’ummar Sudan ciki, ‘yan ƙasar sun haɗa kai wajen yaƙar RSF, yana mai cewa babu wani ɗan Sudan da rikicin bai shafe shi ba ta wata hanya. (TRT Hausa)

Game da ƙoƙarin shiga tsakani na ƙasashen duniya, Burhan ya ce Sudan ta amince Turkiyya ko Qatar su taka rawa, tare da yiwuwar Saudiyya da Masar su ma su taimaka, amma RSF ta yi watsi da waɗannan yunƙuri. (TRT Hausa)

Ya kuma jaddada cewa RSF ba ta da ƙarfi daidai da rundunar sojin Sudan, yana zargin ƙungiyar da ci gaba da kai hare-hare da shigar da makamai cikin ƙasar, musamman a yankin Darfur, duk da matakan Majalisar Dinkin Duniya. (TRT Hausa)

Yaƙin basasa a Sudan ya ɓarke ne tun watan Afrilun 2023 tsakanin sojojin gwamnati da RSF, rikicin da ya jefa ƙasar cikin mummunar matsalar jinƙai, inda dubban mutane suka mutu, yayin da miliyoyi suka rasa muhallansu. (TRT Hausa)

 
 
 
 
 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#