Sport
Dollar
40,5839
0.02 %Euro
46,9354
0.1 %Gram Gold
4.337,4200
-0.06 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Wata doka da ba a saba jin ta ba ita ce ta tilasta wa United saka sanarwar togaciya ga masu sayayya a shagonta.
Babban shagon sayar da kayayyakin ƙwallo na Manchester United ya sanar da haramta buga sunan Cristiano Ronaldo a sabuwar jesin ƙungiyar.
Baya ga tsohon tauraron ɗan wasan nata, United ta kuma haramta buga sunayen wasu tsaffin taurarin ƙungiyar biyu, David Beckham da Eric Cantona.
Hakan ya samo asali ne saboda wata doka da ba a saba jin ta ba, wadda ta tilastawa ƙungiyar saka sanarwar togaciya ga masu sayayya a shagonta.
A watan nan ne Man United ta saki samfuran rigunan da ‘yan wasanta za su yi amfani da su a kaka mai zuwa ta 2025-26.
Kamar yadda aka saba, masoya ƙungiyar sun yi tururuwa don sayen sabuwar jesin. Sai dai da zuwan masu sayayya sai suka ci karo da wannan sanarwar a shagon United.
Saƙo ga masu sayayya
Sanarwar na cewa “Sakamakon wasu takunkumai, ba za mu iya buga sunayen Cantona, Beckham, da Ronaldo ba."
Daga bisani Manchester United ta fayyace cewa taurarinta uku sun mallaki haƙƙin sunayensu, wanda ke nufin ƙungiyar ba za ta iya rubuta sunayensu kan rigunan da take sayarwa ba.
Cristiano Ronaldo da sauran taurarin biyu sun kwashe shekaru a ƙungiyar kuma sun yi tashe, baya ga lashe kofuna da kyaututtuka a zamanin koci Sir Alex Ferguson.
Shi Ronaldo ya taɓa dawowa ƙungiyar a 2021, amma bai daɗe ba bayan samun saɓani da kocin lokacin, Erik ten Hag.
Comments
No comments Yet
Comment