Putin ya bayyana hakan ne yayin taron ƙoli na uku tsakanin Rasha da Afirka da ake gudanarwa a birnin Moscow, babban birnin Rasha.

Putin ya ce Rasha ta fi Ƙasashen Yamma masu 'mulkin mallaka' zama abokiyar hulɗar gaskiya ga Afirka

Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya shaida wa shugabannin Afirka a ranar Laraba cewa Rasha ce abokiyar hulɗa mafi dacewa ga nahiyar, inda ya zargi ƙasashen Yamma da yake kira masu mulkin mallaka da ci gaba da ƙoƙarin cin gajiyar albarkatun nahiyar da kuma amfani da bashi wajen kawo cikas ga ci gabanta.

Putin ya bayyana hakan ne yayin taron ƙoli na uku tsakanin Rasha da Afirka da ake gudanarwa a birnin Moscow, babban birnin Rasha.

Taron na tsawon kwanaki biyu, kuma ya samu halartar shugabannin Afirka da tawagogin gwamnatoci daga ƙasashe 48.

Ana sa ran Putin zai gudanar da tattaunawa ta musamman da da dama daga cikin shugabannin Afirka 22 da suka halarci taron, kan batutuwa da suka haɗa da kasuwanci, tsaro, yarjejeniyoyin sayar da makamai da samar da hatsi.

Taron, wanda aka fara gudanarwa a shekarar 2019, na daga cikin ƙoƙarin Rasha na ƙarfafa haɗin gwiwar siyasa, tattalin arziki da soja da ƙasashen Afirka.

Putin ya shaida wa mahalarta taron cewa:

“Afirka na ƙara tabbatar da matsayinta a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu taka rawa a tattalin arzikin duniya da siyasa.

“Sai dai kafa duniya mai cibiyoyin iko da dama ba abu ne mai sauƙi ba, domin akwai ƙalubale daga ƙasashen da ba su shirya amincewa da wannan sabon yanayi ba, waɗanda suka saba tunani bisa tsohon tarihinsu na mulkin mallaka da kuma tara dimbin dukiya.”

Ya kuma yi magana kan abin da ya kira ƙoƙarin ƙasashen Yamma na mayar da Afirka cikin kangin bashi, tare da tilasta mata karɓar muhimman kuɗaɗen tallafi ko lamuni bisa sharuɗɗan da ke cutar da ita. A cewarsa, irin waɗannan matakai na kawo cikas ga ci gaban nahiyar na dogon lokaci.

Raba ƙwarewa da fasaha

A wani ɓangare na jawabinsa, Putin ya ce Rasha a shirye take ta raba ƙwarewarta da Afirka, ciki har da fasahar zamani ta dijital, tare da taimaka wa ƙasashen nahiyar wajen kafa masana'antun sarrafa albarkatu a cikin gida, maimakon sayen albarkatun ƙasa kawai.

Putin ya ce: “Kamfanoninmu ba sa cin zarafin albarkatun ƙasa da na ɗan Adam ta hanyar cin gajiyar su kamar yadda ake yi a tsarin mulkin mallaka na zamani.

“Maimakon haka, suna faɗaɗa sarrafa albarkatun ƙasa a cikin ƙasashen da ake haƙo su, ta haka ake samar da sabbin ayyukan yi da ƙara kuɗaɗen haraji da gwamnati ke samu.”

Putin ya kuma bayyana cewa Rasha na goyon bayan ƙara tasirin Afirka a cikin Hukumar Lamuni ta Duniya (IMF) da Bankin Duniya.

Ya ce ƙasarsa a shirye take ta fara ayyukan haɗin gwiwa da Afirka wajen gina ababen more rayuwa na sufuri da noma.

Ya ƙara da cewa adadin ’yan Afirka da ke karatu a jami'o'in Rasha ya kai wani sabon matsayi, inda kusan ɗalibai 40,000 ke karatu a jami'o'in ƙasar a halin yanzu.

Putin ya kuma ce Moscow a shirye take ta samar da hatsi da takin zamani ga ƙarin ƙasashen Afirka, fiye da ƙasashe 40 da a halin yanzu suke karɓar kayayyakin daga Rasha.

A cewarsa, Rasha ta samar wa Afirka kayayyakin noma masu nauyin tan miliyan 13 a cikin watanni tara na farkon wannan shekara kaɗai.

#