Dollar

42,8515

0.01 %

Euro

50,9195

0.01 %

Gram Gold

6.170,8800

0 %

Quarter Gold

10.216,8600

-0.28 %

Silver

99,0800

0.11 %

Da yake jawabi a wani taron manema labarai a ƙarshen mako a Kano, Shugaban Hukumar Kwastam, Bashir Adeniyi ya ce ƙwacen ya biyo bayan ayyukan leƙen asiri da aka gudanar ne a cikin rubu’i na biyu da na huɗu na shekarar 2025.

Kwastam ta kama kwantena 20 da aka karkatar da su ɗauke da kayan N769.5m a yankin Kano-Jigawa

Jami’an hukumar fasa-ƙwauri ta Nijeriya, NCS sun kama wasu kwantenoni 20 da aka karkatar da su ɗauke da kayayyakin da darajar kuɗinsu ta kai naira miliyan 769.5 a faɗin yankunan jihohin Kano da Jigawa.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai a ƙarshen mako a Kano, Shugaban Hukumar Kwastam, Bashir Adeniyi ya ce ƙwacen ya biyo bayan ayyukan leƙen asiri da aka gudanar ne a cikin rubu’i na biyu da na huɗu na shekarar 2025.

Ya alaƙanta nasarar da aka samu ɗin da sakamakon binciken bayanan sirri da na aka gudanar da nufin tarwatsa wani gungu da ke shirya karkatar da kwantenoni a manyan titunan ƙasar.

Adeniyi ya bayyana karkatar da kwantena a matsayin babban laifin tattalin arziki wanda ke da illa kan tattara haraji na ƙasa da tsaro da sahihancin Nijeriya a kasuwancin ƙasa da ƙasa.

"Karkatar da kaya babban laifi ne da ke lalata kudaden shiga na gwamnati, yana kawo cikas ga tsaron kasa, kuma yana ɓata matsayin Nijeriya a harkokin kasuwanci na duniya.

Hukumar Kwastam ta Nijeriya ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar dukkan matakan da suka dace don ganowa da daƙile, da kuma hukunta masu laifi," in ji shi.

An gano cewa kwantenonin da aka kama sun ƙunshi kayayyaki iri-iri, ciki har da tayal ɗin da aka yi amfani da su ba bisa ƙa'ida ba da aka karkatar da su daga Yankin Ciniki Marar Shinge na Kano wanda darajarsu ta kai naira miliyan 228.6, da man injin dizal, da kayan sawa da aka yi amfani da su, da yadudduka da leshi da kayan asibiti da ruwan Zamzam na kwalba. 

Hukumar Kwastam ta lura cewa wasu daga cikin kayayyakin sun faɗa ƙarƙashin waɗanda aka haramta shiga da su Nijeriya, kamar yadda aka bayyana a cikin ƙa'idodin Tsarin Haraji na Waje na gama gari (CET).

Adeniyi ya ci gaba da bayyana cewa yayin da daya daga cikin kwantenonin da aka kama ke tsare har zuwa lokacin da za a kammala bin matakan shari'a, an miƙa kwantena biyu cike da kayan magani ga Gwamnatin Tarayya bayan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya, Sashen Kano, ta yanke a ranar 10 ga Disamban 2025.

Ya kuma tabbatar da kama, gurfanarwa, da kuma yanke wa wani Abdulrahman Sani Adam hukunci kan karkatar da kwantena.

An yanke masa hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari tare da zabin tarar naira miliyan uku, wani ci gaba da Shugaban Kwastam ta bayyana a matsayin wani babban abin da zai hana masu yi wa tattalin arziki zagon kasa.

 

 

 

 

A wani mataki na ƙara ƙarfafa kula da jigilar kaya a duk faɗin ƙasar, Adeniyi ya sanar da cewa an kusa kammala aikin samar da na'urorin bin diddigin kwantena na lantarki a faɗin ƙasar.

Ya bayyana cewa fasahar ta ba da damar sa ido kan kwantena a ainihin lokaci, tabbatar da bin ƙa'idodin hanya, da kuma haifar da faɗakarwa idan aka samu matsala daga tashoshin jiragen ruwa zuwa wuraren da ke cikin ƙasa.

 

Da yake sake jaddada alƙawarin Hukumar na kare kudaden shiga, sauƙaƙe kasuwanci, da tsaron kan iyakoki, Adeniyi ya yi gargaɗin cewa masu fasa-kwauri da abokan hulɗarsu za su fuskanci shari'a da ƙwace kayayyaki, da kuma asarar damar kasuwanci.

Ya yi kira ga masu shigo da kaya, wakilan share-fage, da masu kula da sufuri da su bi ƙa'idodin sufuri da aka amince da su sosai kuma su kai rahoton duk wani aiki da ake zargi ga hukumar Kwastam mafi kusa.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#