Dollar

42,8515

0.01 %

Euro

50,9195

0.01 %

Gram Gold

6.170,8800

0 %

Quarter Gold

10.216,8600

-0.28 %

Silver

99,0800

0.11 %

Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya yi magana game da lamarin, yana mai kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu tare da tabbatar musu da cewa an shawo kan gobarar.

Gobara ta lalata katafaren ginin GNI mai hawa 22 da wasu da ke jikinsa a Lagos

A ranar Kirsimeti a Nijeriya, masu ba da agajin gaggawa sun fuskanci ƙalubale mai girma yayin da suke ƙoƙarin kashe wata gagarumar gobara da ta tashi a katafaren ginin Ofishin Inshorar Nijeriya mai hawa 22 da ke kan titin Martins a birnin Legas.

Gobarar, wadda ta tashi a yammacin Laraba 24 ga Disamba, ta bazu zuwa akalla gine-gine huɗu da ke maƙwabtaka, lamarin da ya haifar da yin gaggawar daƙile ta daga hukumomin yankin.

Wutar ta gawurta tare da watsuwa sosai

Rahotanni sun ce gobarar ta tashi da misalin karfe 5 na yamma a hawa na huɗu ko na biyar na ginin, wanda galibi yake aiki a matsayin ma'ajiyar kaya da kuma wurin sayar da tufafi.

Bayanan da aka samu daga ganau da kuma bidiyon da Gidan Talabijin ta Najeriya (NTA) ya nuna sun nuna hayaki mai kauri yana tashi daga benaye da yawa, tare da ganin harshen wuta yana tsiri daga nesa.

Gobarar ta ci gaba da ci har fiye da awanni 10, inda ta yi barna a daya daga cikin gundumomin kasuwanci mafi cunkoso a Legas.

Matsalolin da aka ci karo da su yayin kashe wutar

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA) ta ruwaito cewa gobarar ta yi tsanani a kan benaye da dama, wanda hakan ya kawo cikas ga kokarin kashe ta saboda hayaki mai kauri da kuma zafi mai yawa.

Sakataren dindindin na LASEMA, Olufemi Oke-Osanyintolu, ya yi gargadi game da barazanar da ka iya tasowa ga rayuka, gine-gine da ke kusa, da kasuwanci, yana mai kira ga jama'a da su fice daga yankin nan take domin guje wa asarar rayuka sakamakon shakar hayaki.

"Gobarar ta ci gaba da yaduwa, inda ake bukatar ci gaba da hadin gwiwa tsakanin hukumomi da kayan aiki na musamman don hana fantsamarta," in ji Oke-Osanyintolu, yana mai jaddada muhimmancin lamarin.

Matakan ceto

Ganin yadda gobarar ke ƙara ta'azzara, an tura ƙungiyoyin gaggawa, ciki har da Sashen Gaggawa na Shark na LASEMA, Hukumar Kashe Gobara da Ceto ta Jihar Legas, da motocin asibiti duk don aikin kashe gobara da ceto.

Hukumomin tsaro sun killace yankin don takaita shiga, suna tabbatar da tsaron lafiyar jama'a da ma'aikatan gaggawa.

Rahotannin sun nuna cewa gobarar ta shafi akalla gine-gine huɗu da ke kusa da wurin, ciki har da coci da masallaci.

Mazauna da masu kasuwanci a yankin ba su iya barci ba saboda fargaba da tantance barnar da asarar da aka yi.

Martanin gwamnati da tabbaci

Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya yi magana game da lamarin, yana mai kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu tare da tabbatar musu da cewa an shawo kan gobarar.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Dabaru, Gbenga Omotoso ya fitar, gwamnati ta tabbatar da cewa ba a samu rahoton asarar rayuka ba, duk da cewa har yanzu ba a tantance musabbabin gobarar ba.

An sami kiran gaggawa game da gobarar da misalin karfe 4:41 na yamma, wanda ya haifar daukar mataki nan take daga masu kashe gobara da ke aiki a tashoshin kashe gobara na Ebute Elefun da Dolphin, tare da ƙarin tallafi daga Ofishin Kashe Gobara na Sari Iganmu da hedikwatar Alausa.

Jami'an kashe gobara sun isa wurin cikin mintuna 12 kuma sun fara ayyukan dakile gobarar.

Ana bincike

Binciken farko ya nuna cewa gobarar ta samo asali ne daga hawa na biyar na ginin, wanda ya sauya daga ofishin kamfani zuwa wata ma'ajiyar kaya da cibiyar sayar da tufafi.

Gwamna Sanwo-Olu ya sa ido kan lamarin a duk tsawon dare, yana ci gaba da magana da masu ba da agajin gaggawa da hukumomin tsaro akai-akai .

Da misalin karfe 3:40 na safe, an shawo kan gobarar sosai, kuma gwamnan ya ci gaba da samun sabbin bayanai da kuma bayar da umarni.

"Babban abin da muka sa a gaba shi ne tsaron rayuka; na ba da umarnin a tabbatar da tsaron ginin da kewayensa sosai, kuma dole ne ma'aikatan gaggawa su tabbatar da cewa babu wanda ya rage a ciki," in ji shi.

Gwamnan ya yaba wa masu kashe gobara da masu bayar da agajin gaggawa saboda gaggawa da jarumtakar da suka nuna wajen magance lamarin.

"Ya kamata 'yan Lagos su kwantar da hankalinsu; an shawo kan lamarin," ya tabbatar wa jama'a.

Matakan kariya don gaba

Hukumomi sun fara tantance lafiyar gine-ginen da ke kusa domin hana afkuwar wani abu na biyu, tare da sa ran samun ƙarin bayani yayin da ake ci gaba da bincike kan musabbabin gobarar.

Lamarin ya zama abin tunatarwa mai ƙarfi game da mahimmancin shirye-shiryen gaggawa da kuma mayar daukar matakan ko-ta-kwana a birane, musamman a wuraren kasuwanci masu yawan jama'a kamar Legas.

Yayin da al'umma ke fara murmurewa daga wannan mummunan lamari, abin da aka fi mayar da hankali a kai shi ne tabbatar da tsaro da kuma hana afkuwar wani abu mai kama da haka a nan gaba.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#