Dollar

0,0000

%

Euro

0,0000

%

Gram Gold

0,0000

%

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Tun a Afrilun 2025 ne aka miƙa koke kan harin da fararen hula 13 suka halaka, sannan mutum takwas suka jikkata.

Rundunar sojin Nijeriya ta biya diyya ga wadanda harin sama ya rutsa da su a Sokoto

Rundunar Sojin Saman Nijeriya (NAF) ta biya diyya ga dangogin waɗanda harin kuskure na sojin ya shafa ranar 25 ga Disamban 2024, a ƙauyukan Gidan Bisa da Rumtuwa na ƙaramar hukumar Silame a jihar Sokoto.

Babban Jami’in Yaɗa Labarai na Sojin, Air Vice Marshal Edward Gabkwet ne ya gabatar da diyyar yayin wata ziyara da ya kai a madadin babban hafsan sojin saman Nijeriya, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke.

Ya bayyana yabawarsa ga gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu bisa kyakkyawar tarba da cigaba da ba wa sojin haɗin-kai daga gwamnatin jihar.

Da yake jawabi kan yanayin da ya haifar da lamarin, jami’in ya ce an kai harin ne ƙarƙashin shirin “Fansan Yamma” bayan samun bayanan sirri da ke nuna giftawar ‘yanta’adda ta cikin yankunan da abin ya shafa.

Bayan harin, an miƙa koke a Afrilun 2025, wanda ya janyo bincike kan harin, inda aka gano fararen hula 13 sun halaka, sannan mutum takwas sun jikkata. Jami’in sojin ya bayyana abin da cewa mai baƙanta rai kuma rundunar sojin ta amsa laifi.

Da yake mai da jawabi, gwamnan Sokoto ya yaba wa Rundunar Sojin Saman kan nuna ƙwarewa, nuna gaskiya, da kuma tausayi.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#