Dollar

0,0000

%

Euro

0,0000

%

Gram Gold

0,0000

%

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Amma kasancewar waɗannan jiragen a Afirka ta Yamma sun biyo bayan barazanar Shugaban Amurka Donald Trump a watan Nuwamba na shiga Nijeriya da sojoji saboda abin da ya ce gazawar ƙasar wajen “hana zaluntar Kiristoci.”

Jiragen Amurka na nazarta da tattara bayanan sirri kan Nijeriya bayan barazanar Trump: Reuters

Jiragen saman Amurka sun fara gudanar da zirga-zirga don yin nazari da tattara bayanan sirri a manyan sassan Nijeriya tun daga karshen watan Nuwamba, a cewar bayanan bin diddigin jiragen sama da kuma jami'an Amurka na yanzu da ma tsoffin jami'ai, a wata alama da ke nuna karuwar hadin gwiwar tsaro tsakanin kasashen.

Reuters ba ta iya tantance irin bayanan da waɗannan jirage ke neman samu ba.

Amma kasancewar waɗannan jiragen a Afirka ta Yamma sun biyo bayan barazanar Shugaban Amurka Donald Trump a watan Nuwamba na shiga Nijeriya da sojoji saboda abin da ya ce gazawar ƙasar wajen “hana zaluntar Kiristoci.”

Bayanan bin diddigin jiragen na watan Disamba sun nuna cewa jiragen da wani kamfanin kwangila na Amurka ke sarrafawa waɗanda ake amfani da su wajen leken asiri galibi suna tashi daga Ghana, su ratsa sararin samaniyar Nijeriya kafin su koma Accra, babban birnin Ghana.

Jiragen leƙen asiri

Bayanan bin diddigin jirage sun nuna cewa kamfanin da ke kula da su shi ne Tenax Aerospace da ke Mississippi, kamfani mai samar da jiragen aiki na musamman wanda ke aiki kafada da kafada da sojojin Amurka, in ji shafin intanet na kamfanin.

Sai dai kamfanin Tenax Aerospace bai mayar da martani ga buƙatar yin sharhi da ake nema daga wajensa ba.

Liam Karr, shugaban shirin Critical Threats na tawagar Afirka, ƙarƙshin cibiyar American Enterprise Institute, ya yi nazarin bayanan jiragen.

Ya ce aikin yana kama da ana gudanar da shi daga filin jirgin sama a Accra, wanda ke matsayin cibiyar sadarwar kayan aiki ta sojojin Amurka a Afirka.

Karr ya ce wannan aiki alama ce ta farko da Amurka ke sake gina ƙarfinta a yankin bayan da Nijar ta umarci sojojin Amurka da su bar wani sabon sansanin sojin sama da aka gina a kasar a bara.

"A cikin 'yan makonnin nan mun ga sake dawo da zirga-zirgar jiragen leken asiri da sa ido a Nijeriya," in ji Karr a wata hira da aka yi da shi.

Taro mai ma’ana

Wani tsohon jami'in Amurka ya ce jirgin daya ne daga cikin kadarori da gwamnatin Trump ta mayar da su Ghana a watan Nuwamba. Ba a bayyana adadin jiragen da suka rage a Ghana ba.

Wani jami'in Amurka na yanzu ya tabbatar cewa jirgin yana shawagi a samaniyar Nijeriya amma ya ƙi bayar da cikakkun bayanai saboda hankali taka tsantsan na diflomasiyya a kan batun.

A cikin wata sanarwa, Pentagon ya ce gwamnatin Amurka ta gudanar da taruka masu amfani da Nijeriya bayan saƙon Trump game da ƙasar, amma ya ƙi tattaunawa kan al'amuran leken asiri.

Mai magana da yawun sojojin Nijeriya bai ce komai ba bayan tuntuɓarsa kan yin magana a kan batun.

Mataimakin Ministan Tsaron Ghana ma bai mayar da martani ga buƙatar sharhi ba.

Suna shawagi samaniyar Nijeriya kusan kowace rana

Wani ma'aikacin tsaro na Nijeriya, wanda ya yi magana a ƙarƙashin sharuɗɗan rashin bayyana sunansa, ya ce Amurka ta amince a taron 20 ga Nuwamba tsakanin Mashawarcin Tsaro na Ƙasa na Nijeriya Nuhu Ribadu da Sakataren Tsaron Amurka Pete Hegseth na tura jiragen sama don tattara bayanai.

Mai magana da yawun sojojin Nijeriya bai mayar da martani ga buƙatun sharhi ba.

Bayanan bin jirage sun nuna an ga jirgin Tenax Aerospace a ranar 7 ga Nuwamba a MacDill Air Force Base, wanda ke masaukin hedkwatar United States Special Operations Command a Tampa, Florida.

Ya tashi zuwa Ghana a ranar 24 ga Nuwamba, 'yan kwanaki bayan taron manyan jami'an tsaro na Amurka da Nijeriya, a cewar bayanan bin jiragen.

Bayanin ya nuna cewa jirgin ya ratsa saman Nijeriya kusan kowace rana tun farkon aikin.

Jirgin nau'in Gulfstream V ne, wani jirgin kasuwanci mai nisan tafiya mai yawa wanda akai-akai ake gyarawa don aikace-aikacen leken asiri, sa ido da tattara bayanai, a cewar bayanan.

Gaggawar tsaro

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ayyana gaggawar tsaro a watan da ya gabata ya kuma umarci sojoji da 'yansanda su fara daukar ma'aikata da yawa don magance tabarbarewar tsaro a fadin ƙasar.

Wannan matakin ya biyo bayan hare-hare a jihohi da dama na Nijeriya inda fararen-hula suka rasa rayukansu aka kuma sace wasu, da kuma gagarumar satar fiye da yara ‘yan makaranta 300 a arewacin Nijeriya.

Amurka da Nijeriya sun kafa ƙungiyar aiki tare don yin aiki kan tsaro, a cewar ɗan majalisar wakilai na jam'iyyar Republican Riley Moore, wanda kwanan nan ya ziyarci wannan ƙasa ta Afirka ta Yamma.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#